Wannan shi ne jawabin Jagoran Harkar Musulunci, Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) kan abubuwan da ke faruwa a Yemen, Ya yi jawabin ne a gidansa da ke Abuja, 7 ga February 2022
Assalamu alaikum wa rahmatullah, wa barakatahu.
"Zan so na yi tsokaci dangane da abubuwan da ke faruwa a Yemen, ba wai na dauki abu daya ne da zan magana a kai ba, zan yi ne gaba daya akan abubuwan da ke faruwa. Yanzu shekara bakwai kenan Yemen na fuskantar hare-hare, a abun da aka kira wai ‘yaqi’. Ma'anar ‘yaqi’ shi ne fada tsakanin bangaren sojojin kasashe biyu.
"Amma abun da ke faruwa a Yemen ba yaqi ba ne sam, kisan kai ne, ta'addanci ne. Ana kai hare-hare da kuma yin ruwan wuta a kan fararen hula, a kashe mata, yara da maza har a wuraren aikin su.
"Sun kai hare-hare a makarantu, wanda ya yi sanadiyar rasa rayukan malaman makaranta da dalibai, har motar makaranta dauke da dalibai ma sun kai mata hari, haka ma gidajen yari, harin har a asibitoci, sun kashe majinyata, da ma'aikatan kiwon lafiya.
"Mutum zai iya tambaya: shin wannan yaqi ne? Menene manufar yin duk wadannan hare-haren? Me yasa a ke afka wa al’ummar Yemen? Su masu aiwatar da harin, gamayyar masarautar Saudiya (KSA) da kuma hadaddiyar daular larabawa (UAE), bisa umurnin iyayen gidansu Amerika, Birtaniya, da Faransa sun ce wai dalilin harin shi ne dawo da korarren shugaban qasar Yemen, Mista Hadi kan kujerar mulki. Mutum zai iya tambaya a nan, shin aikin wadannan kasashen ne zabar wa Yemen wanda zai zama shugaban kasar su? Mutanen Yemen ke da iko da 'yancin zabar wa kansu shugaban kasa. Idan suna son sa (Mr. Hadi) su ne za su dawo da shi, idan kuma ba su son shi, shikenan ra’ayin su ne.
"To ma wai, ya za ka yi tunanin share mutanen wata kasa saboda dawo da mutum daya kan kujerar mulki, to idan ma ka dawo da shi din, zai mulki gawarwakin mutane ne? Ko kuma zai shugabanci ragowar yaqi ne da ke alhinin rasa yan uwan su da iyalan su? Misali, zai yiwu yaran da aka kashe iyayen su, su amince da wanda (ta sanadin shi aka kashe iyayen su) a matsayin shugaban kasa? Ko kuma za ka yi tunanin iyayen da a ka kashe ‘ya yan su (domin dawo da Hadi kan mulki) za su goyi bayan (Hadi) ya zama shugaban kasa? Ba hankali sam a cikin wannan abin da su ka kira da suna wai ‘yaqi’, fada ne na rashin kan gado.
"Mutum zai iya tambaya, menene dalilin da ya sa ake wannan? Lallai ba zai zama domin mayar da wani kan mulki ba, dole akwai wani dalili. Wani abu ma, su hadakar (masarautar Saudiyya da hadaddiyar daular larabawa) ana ingiza su ne, domin duk makaman da Saudiya da kawayenta su ke anfani wurin kai hare-haren, na kasashen yammacin duniya ne, da makamansu da ma'aikatansu a ke yin duk abinda a ke na hare-hare kan al'ummar Yeman."
"Mutum zai iya tambaya, me yasa turawan yamma ke son mamaye Yemen da ruguza ta? Sun aikata haka a wasu kasashen kamar Libya, Iraq, da Syria, yanzu kuma a Yemen su ke yi, su na son ta kowane hali sai sun rugurguza duk wani abu da za su iya a kasar. Ya yi kama da akwai wani tsarraren shiri na samar da abun da su ka kira 'sabuwar duniya' (ko kuma babbar kasar Isra'ila), kuma a haqiqa su na daukan kasashen da ke cikin wannan hadakar a matsayin wani bangare na ‘’babbar Isra’ila’ (da su ke burin samarwa).
"Kasar Jordan dama tare ta ke da su, suna kallon idan wani abu ya taso za su yi fada a tsakaninsu, su kashe kansu, su yi rauni, don haka daga karshe cikin sauki su (ma’abota dagawar duniya) za su iya wanke su daga duk wani zargi.
"Me yasa duniya ta yi shiru kan abun da ke faruwa a Yemen na ta'addanci? Ga rashin ruwan sha mai kyau, ga matslar lantarki, da kuma wutar injinonin amfani a wurare ciki har da asibitoci, kasar da ke fama da matsalar rashin kayan jinkai tun a baya, yanzu hare-haren ya kara tsananta al'amurra, zuwan cutar Covid-19 kuma ya kara tsananta masu yanayi, sun zama karkashin mamaya, an hana shiga da abinci, magani da duk wani abu. Kuma a haka su a ke kira masu laifi. Su masu aikata laifin (na haqiqa) su ke zargin Yemen da aikata laif- laifin da sam ba su taba aikatawa ba.
"Nau’in ta’addanci da kuma karancin kayan jin kai da tassarufi da Yemen ke fuskanta shi ne irin shi mafi muni da ya taba faruwa a wannan zamanin, (mutane) kuma kamar ba su damu ba. Amman dai Alhamdulillah, su al'ummar Yeman sun dake kyam, kuma su na da yancin yin hakan. A yayin da hare-haren mayar da martani da sojojin Yeman ke kai wa mafi yawa a kan sansanin sojojin hadakar kasashen ne, su kuwa hadakar su na kai hare-haren ne kan fararen hula. (Al’ummar Yemen) sun dake, kuma ba su daina fafutikar (neman haqqin su) ba.
"Muna fata tare da rokon nasara ta kasance tare da mutanen Yemen insha Allah. Allah Ya ba al'ummar Yeman kariya, Allah Ya rusa ma’abota dagawar duniya da kuma karnukan farautar su da ke yin yakin a madadin su.
"Amincin Allah Ya tabbata ga Manzo da iyalan gidansa tsarkaka."
Fassara: Al-Mansoor Translation Team
EmIl: almansoortranslationteam@gmail.com
Tags
Jawaban Jagora
Labbaika ya Al zakzaky
ReplyDeleteLabbaika ya sayyid (h)
ReplyDelete