Ni sunana Muntazar Abububakar Abdullahi Sakkwato. Shekaruna 13. Lokacin da sojoji suka Kai wa yan'uwa hari ina Husainiyya Bakiyyatullah, muna ciki. Daman ranar akwai bikin sanya tuta, sai muka ji hayaniya a waje aka ce sojojine suka zo. Muna nan ba mu san me ke faruwa ba, sai muka ji an ce sun kewaye Husainiyya gaba daya kuma ga alama za su yi harbi ne. Sai 'yan'uwan da ke ciki har da mu aka fito ana kabbara. Sai suka fara harbin yan'uwa. Sun kashe 'yan'uwa da dama a lokacin, sun kuma ji wa wasu rauni. Haka dai muka ci gaba da kabbara suna harbi har Magriba. Da dare ya yi ana addu'a, ana kuma diban wadanda suka harba. Mun dauka sun wuce, sai mukaji suna cewa a fito ayi saranda ba za su taba kowa ba, sai aka kyale Su, domin mun san yaudara ce. Domin a nan ma da wasu da suka fito a inda suke, duk sun harbe su.
Muna ciki tun da safe ba wurin fita, sun zagaye Husainiyya. Da dare sai aka zo da wani abinci, bai da ya aka ce mu da muke kanana mu zo, aka ce amma kowa diba daya zai yi ya sa a bakinsa. Da Asuba wasu ba su kai ga yin Sallah ba, sai muka ji sun fara harbi. Muka tashi muka kabbara, sai muka ji harbin da suke ya karu. Yan'uwa suna tunanin ya za a yi? Sai aka ji sun fara harbo gurneti cikin Husainıyya, wuta ta kama, kuma ga hayaki ba ka ganin ko'ina. Sai ma suka shigo cikin Husainiyya din suka fara harbin 'yan uwa suna kashe masu rauni.
Da abin ya tsananta, Sai aka ga mu da muke kanana, aka ce a tsalakar da mu daya gidan da ke kusa da Husainiyya. Ashe lokacin da ake tsallawa damu, wasu daga cikin soJojin sun kula, sai suka shigo gidan, sai muka haura ta wani waje, a nan ma muka ji sun shigo suna dubawa daki-daki, Sai muka Ji suna cewa wasu yara da muke tare cewa su fita ko su harbe su, suna fitowa daidai lokacin wani soja ya shigo, sai muka ga ya harbi wasu daga cikin su a kafafuwa, Muna kallo muka ga sun harbi wani yaro, nan take muka ga ya fadi Kasa. Ganin in sun matso za su gan mu, sai muka fita muka sami wani rami da ba a zaton wani zai shiga ciki muka shiga ciki muka buya. Kwananmu uku a ciki. Yini na hudu ne muka ga zamanmu a nan ba zai yiwu ba, tunda ba ci, ba sha, kuma mun daina jin wata hayaniya, sai muka fito muka leka, sai muka hangi tankar sojoji, amma sun janye ta tana nesa da mu. Sai muka rabu dai-dai don kada su gane mu, muka tsallaka titi, sai muka duka muka ruga a guje. Suka harbo mu, Allah ya kiyaye ba su samu ko daya a cikin mu ba. Sai ni na zagaya na je unguwar da muke zaune, shi ne Mahaifina ya dauko ni muka dawo nan gida Sakkwato.
Lokacin da muka buya a rami mu hudu ne, ba su kama ko daya a cikin mu ba. Tsawon wadannan kwanakin
da na yi ba a gan ni ba, kilan iyayena sun zaci na bata ne ko nayi shahada, amma dai ita Yayata Nusaiba Abubakar sojoji sun harbe ta, ta yi shahada a Gyallesu, gidan Sayyid (H) Tunanina nan gaba dangane da Harka, shi ne muna nan
ba za mu bari ba. Ba za mu daina ba, muma sai munyi shahada.
Tags
Zaria Massacre