Offline

Isra'ila Ta Kashe Ƴan Jarida 6, Anas al-Sharif Tare Da Abokan Aikin Shi 5.

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan 

Isra'ila ta bayyana ƙarara cewa ita ta kashe Anas al-Sharif inda ta tuhume shi da kasancewa ma'aikacin Hamas, sun kashe Anas ne tare da abokan aikin shi guda 5 ta hanyar jefa masu bom a tantin su a birnin Gaza.

Shahararren ɗan jaridar yana aiki da kafar yaɗa labarai ta Aljazeera ne, Isra'ila
ta yi amfani da jirgin yaƙi ta jefa mashi bom tare da abokan shi a daidai lokacin da suke cikin tantin ƴan jarida a asibitin Al-Shifa dake birnin Gaza a jiya Lahadi 10 ga August.



Abokan aikin na Anas su ne, Mohammad al-Khalidi, Muhammad Qureiqaa, Ibrahim Zaher, Moamen Alaywa da kuma Muhammad Nofal, duk an kashe su tare da Anas al-Sharif.

Ofishin yaɗa labarai na gwamnatin Gaza ya bayyana cewa "Zuwa yanzu adadin ƴan jaridar da Isra'ila ta kashe daga fara wannan yaƙi zuwa yanzu ya kai mutum 238" Ofishin ya bayyana haka ne a yau Litinin bayan an sanar da shahadar su Anas al-Sharif a jiya.

"Mun ɗora ma Isra'ila, da Amurka, Burtaniya, Faransa da Jamus masu taimaka ma ta wajen wannan aika aika alhakin wannan kisan kiyashin, muna kira ga al'ummar duniya da ƙungiyoyi da duk wanda ya damu da kisan masu aikin media da ƴan jarida su fito su ƙalubalanci wannan aika aikar kuma a gurfanar da makasan nan a kotun duniya a hukunta su" A cewar ofishin.

Anas al-Sharif dai ya kasance yana aikin yaɗa ta'addancin Isra'ila tun daga fara wannan yaƙin a shekarar 2023, bisa wannan ne Isra'ila ta tuhume shi da kasancewa ma'aikacin Hamas saboda yana tona ma su asiri, a cewar Isra'ila wai yana yi ma Hamas aiki a bangaren harba rokoki.


"Ɗan Ta'adda Anas al-Sharif shugaban wani rukuni ne a kungiyar Hamas kuma suna shirin harba rokoki kan fararen hula a Isra'ila" A wani bayani da sojin Isra'ila suka fitar domin tabbatar da cewa su suka kashe shi a matsayin dalilin kisan.

Tun a shekarar da ta gabata ne dai Isra'ila ta fitar da wasu takardu inda take nuna cewa Anas al-Sharif yana da alaka da rundunar "Qassam Brigade East Jabalia Battalion" ta ƙungiyar Hamas.

Har ila yau a cikin takardun sun bayyana sunan ɗan jaridar Aljazeera Hosam Shabat wanda suka kashe tun watan March cewa shi ma yana da alaka da kungiyar ta Hamas.

A watan July da ya gabata Anas al-Sharif ya fitar da wani gargadi inda yake cewa "Sojin Isra'ila suna yi man barazana saboda aikin da na ke yi na Jarida a Aljazeera" ya kara da cewa "Ni Anas ɗan jarida ne bani da alaƙar siyasa da wani bangare, abinda na sa gaba kawai shi ne kawo rahotonnin gaskiyar abinda yake faruwa, a wannan lokaci da Yunwa ke kashe mutanen Gaza faɗin gaskiya ya zama barazana a wurin ƴan mamaya".

Daga ƙarshe dai Isra'ila ta yi nasarar kashe Anas al-Sharif tare da abokan aikin shi domin rufe mummunar aika aikar da suke yi a zirin Gaza.

Post a Comment

Previous Post Next Post