Offline

Gwarazanmu Shahidanmu: Shaheed Qaseem Umar Sokoto

KAFIN WAƘI'AR ALU.
Duk shekara mukan Cinye kyautar mota da ake Sawa a Ranar Yaumush Shuhada'u ga Duk Zone ɗin da sukafi sauke haƙƙin su.

SOKOTO ZONE munzama Mune duk shekara muke lashe wannan gasar kafin waƙi'ar Alu.

Bayan Alu yakama Shaheed Sheikh Qaseem yakaishi gidan yari tsawon shekaru 6, watarana a Yaumush Shuhada Sai su malam Hafizuhullah suke cewa masu cin Mota basanan.

A shekarar da su Malan Qaseem suka samu ƴanci kuma Cikin luɗufin Allah Again mune muka sake lashe Wannan kyautar saboda jajircewar sa, da ganin kowane ɗan uwa yasauke haƙƙin Shuhada, Yakai Shaheed da kansa yake zuwa ƙauye da Birni a Zone ɗinmu Domin karɓan wannan haƙkin na Shuhada.

A Wannan shekarar Bayan kammala Taron, a Zariya yadawo Gida inda yakira Dukkan wakilan ƴan uwa Nakowace Da'ira daya haɗa SOKOTO ZAMFARA KEBBI Harma da wani Yanki Na ƙasar Nijar.

Sai Shaheed Qaseem yake cemasu Nakiraku ne Domin wannan mota da mukasamu Naji menene Ra'ayinku akai me yakamata muyi da ita..?

Wani yace a siyar a rabawa iyalan shaheedai kuÉ—in.
Wani yace ai Malan kawai kaÉ—auka kazanki hawa.
Wani Yace a siyar a siya filaye da kuÉ—in.

Kowane daga cikin wakilan ƴan uwa da Nashi shawarin, bayan sun gama faɗa sai Shaheed yake cemasu Ni kunsan me Nake gani yakamata ayi da ita.? Sukace A'a sai Shaheed yace zamu siyar mukai kuɗin Acigaba da ginin Husainiyya Baƙiyatullah.

Bayan Siyarda motar Shaheed Qaseem yaje gaban su Malan yake cemasu motar da muka samu munsiyar da ita ga kuɗin a ƙara aginin Husainiyya.

Buɗar bakin su Malan Zakzaky baice komai ba Illa ƙasimu kenan sai su Abba sukayi murmushi.

Kunsan meyasa Shaheed Qaseem yace akai kuÉ—in aginin Husainiyya.? saboda yasan haka zai faranta Ran jagora ne Babban Burinsa yayi abinda Zaisaka Sheikh Zakzaky a Farinchiki.

Wannan shine haƙiƙanin mabiyi Amincin Allah agareka ya shaheedul Akhbar Baba Qaseem. 🌹

Nazeer Hassan Shinkafi.
Saturday 27-2-2022.
Yaumush Shuhada.

Post a Comment

Previous Post Next Post