Daga-Bin Muhammad KD
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa kofar tattaunawa da Amurka kan shirinta na makamashin Nukliya a bude take, amma kafin haka sai gwamnatin kasar Amurka ta biya diyyar kura kuran da ta yi a bayan.
A wata hirar da yayi da Jaridar Le Monde na kasar Faransa Aragchi ya kara da cewa da farko Amurka yakamata ta canza halayenta, na rashin kaiwa kasar Iran hare-hare a lokacin tattaunawa.
Ya ce diblomasiyya hanyace mai tituna biyu na zuwa da komawa, amma Trump ya zo ya rufe dayar. Kuma tattaunawar diplomasiyya a wajen Iran a ko yaushe a bude take, hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan kasar Iran a cikin yakin kwanaki 12 keta hurumin diblomasiyya ne, kuma dole Amurka ta biya diyyan Barnan da ta yi. Kuma wannan hakkin Iran ta nemi wannan hakkin.
Hakama kaiwa cibiyan makamashin Nukliya wanda ke karkashin kula na hukumar IAEA kuskure ne. don babu tabbaci daga hukumar kan cewa shirin ya karkata daga na zaman lafiya. Wannan ma sai Amurka ta biyya diyyar yin haka.
