A ƙasashen da suka san mutuncin su da ƙimar ƙasar su, yin turjiya ga ƴan mamaya wajibi, wato wani aiki ne mai tsarki.
Ana ɗaukar ƴan gwagwarmaya a matsayin gwaraza da suka sadaukar da rayukan su wajen samar da tsaro ga rayukan sauran al'umma, dan haka mutane ke ƙimanta gwagwarmaya da haƙƙin su na kare ƙasa.
Sai dai a Lebanon al'amarin ba haka yake ba, a daidai lokacin da haramtacciyar ƙasar Isra'ila ke cigaba da mamaye ƙasar ta Lebanon domin cimma burin ta na kafa "Babbar Isra'ila", ita kuma gwamnatin ƙasar ta Lebanon tana ƙoƙarin ƙwace makaman rundunar Hezbollah. Idan aka karɓe makaman Hezbollah Lebanon ta fuskanci wasu hare hare daga Isra'ila waye zai kare ƙasar ? Shin ƙasashen duniya za su kare Lebanon?
A'a. Lebanon zata fuskanci irin abinda Gaza ke fuskanta ne, za a riƙa tsayawa gaban Camera ana Allah wadai a ƙarƙashin ƙasa kuma ana baiwa ƴan mamaya makamai da taimako, wannan itace gaskiyar abinda zai faru.
MATAKAI BIYU , MAKOMA BIYU
A ranar 5 ga watan August an ƙaddamar da wasu matakai biyu waɗanda za su haifar da makomar Lebanon a fadar mulki ta "Baabda Palace" gwamnati ta sanar da cewa ta ɗora ma sojojin ƙasar alhakin tsara yadda za a raba ƙungiyoyin gwagwarmaya da makaman su, wannan hari ne kai tsaye akan Hezbollah.
Bayan awa ɗaya da sanar da wannan mataki, shugaban ƙungiyar Hezbollah Sheikh Na'im Qasim ya yi wani zazzafan jawabi daga unguwar Haret Hreik dake kudancin Lebanon inda ya yi martani yana mai cewa " Gwagwarmaya ta gwammaci shahada akan ta miƙa makamai ta zauna hannu buɗe babu makaman kare kai a cikin gidaje".
HANNUN AMURKA CIKIN WANNAN YUNKURI
A ƙarƙashin wannan yunƙuri na mahukuntan Lebanon Amurka ce tayi uwa ta yi makarɓiya ta hannun jakadan ta Tom Barrack wanda ke zaune a matsayin mai matsin lamba a maimakon jami'in diplomasiyya. A ranar 4 ga watan August ɗin nan da muke ciki ya yi wani jawabi inda ya wanda aka kira "Third Memorandum" wanda ke ɗauke da neman a karɓe makaman Hezbollah cikin makonni.
Kuma sakamakon rashin yin hakan shine : IMF zata daina baiwa Lebanon kuɗi, za a dakatar da yarjejeniyar bada bashi ta ƙasashen Gulf "Gulf Reconstruction Loans", sannan kuma za a ƙasƙantar da Fasfo "Passport" ɗin ƙasar ta Lebanon a Bizar "Visa" Amurka.
HAƊARIN ABINDA SUKE HANƘORO
Wannan yunƙurin ba kawai batun karɓe makamai bane, a'a mataki ne da zai basu damar yin iko da Lebanon yadda suke so, miƙa ma Amurka wuya mataki da hatta gwamnatin da ta gabata ba ta amince da shi ba duk da ba ta jituwa da Hezbollah.
Wanan mataki miƙa wuya ga Amurka tare da yin watsi da ra'ayin al'ummar Lebanon.
Abun ban mamaki, Amurka da ke baiwa Isra'ila kariya da makamai tana kisan kiyashi a Gaza itace kuma yanzu ta dage sai an karɓe makaman ma su kare ƙasar su.
Yarjejeniyar Ɗa'if "Taif Agreement" wadda ta kawo ƙarshen yaƙin basasar Lebanon a shekarar 1989 ta lamunce yin gwagwarmaya da makami wajen korar Isra'ila, madamar ta mamaye ko ta yi barazana ga iyakokin Lebanon.
Haryanzu wannan ƙa'idar tana nan, tun da haryanzu jiragen leƙen asirin Isra'ila suna shawagi a sararin samaniyar Lebanon, a lokaci guda kuma sojojin Isra'ila suna cikin ƙasar ta Lebanon, Amurka na neman Hezbollah ta ajiye makamai amma ta kasa saka Isra'ila ta ɗabbaƙa yarjejeniyar majalisar dinkin duniya ta 1701 "UN Resolution 1701"
KIRAN A SAKE NAZARTAR WANNAN MATAKI
A cikin jawabin na Sheikh Na'im Qasim ya bayyana cewa kamata ya yi a bamu jadawalin korar ƴan mamaya ba wai a nemi karɓe makamin mu ba"
Sheikh Na'im ya ƙara da cewa a tuna da aƙalla dakarun Hezbollah dubu 5 suka yi shahada daga Oktoban 2023 zuwa yanzu. Bai kamata a nemi ƙwace makaman waɗanda suka bayar da rayukan su domin kare kudancin Lebanon ba, su miƙa wuya ga wannan shirin da Amurka ta tsara.
Wannan jan hankali na Sheikh Na'im an karar wa ce domin a tuna tarihin yaƙin basasar Lebanon wanda ƙasashen waje suka haddasa ta hanyar yin katsalandan a cikin harkokin gudanarwar ƙasar, wannan matakin da gwamnatin ƙasar ta ɗauke yanzu zai sake buɗe tsohon ciwo ne kawai.
Domin tilasta sojojin Lebanon su fuskanci dakarun Hezbollah zai tarwatsa haɗin kan da ya rage ne kawai tsakanin al'ummar ƙasar.
WAYE ZAI AMFANA DA WANNAN MATAKI
Tabbas al'ummar Lebanon ba za su amfana da komai ba, waɗanda za su amfana da karɓe makaman Hezbollah ita ce "Isra'ila" domin za a kawar mata da babbar barazanar soji da take fuskanta, sai kuma Amurka da ƙasashen Larabawa dake ta hanƙoron daidaitawa da Amurka a kawo karshen gwagwarmayar Palasɗinu.
MIƘA WUYA A FAKAICE
Babban abun takaicin shine yadda wasu masu faɗa aji a Lebanon suka matsa lamba, ɗaukar wannan matakin ba iya raunin su ya nuna ba, ya nuna haɗin bakin su da maƙiya a maimakon cijewa da rashin amincewa sai suka yi maraba da matakin, maimakon su tsaya kan cewa lallai Isra'ila sai ta girmama yarjejeniya ta dakata da ta'addancin da take yi sai suka dawo yaƙar masu kare mutuncin ƙasar, lallai wannan ba shugabanci bane miƙa wuya ne.
©️ Mahadi Tukur Almizan & Muhammad Hammoud | ABS Radio
