Offline

Ɗan Gwagwarmaya Fursuna Mafi Daɗewa A Yammacin Turai Zai Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Shekaru 40



 Daga - Mahadi Tukur Almizan 

Kotu Ta Amince a Saki Georges Abdallah Bayan Shekaru 40 a Kurkukun Faransa

An amince da sakin fitaccen jarumi ɗan gwagwarmaya na ƙasar Lebanon, Georges Abdallah, daga gidan yarin Faransa, bayan ya kwashe fiye da shekaru 40 a tsare — wanda ya zama fursunan siyasa mafi daɗewa a kurkukun Yammacin Turai.

A yau 17 ga watan Yuli Ma’aikatar Shari’ar ƙasar Faransa ta sanar cewa wata kotun daukaka kara da ke birnin Paris ta bayar da umarnin a saki Georges Abdallah daga kurkuku ranar 25 ga Yuli, da sharadin cewa ya bar Faransa kuma kada ya sake dawowa har abada.

Ana tsare da Abdallah a kurkukun Lannemezan da ke kudancin Faransa. Majiyar kafar yaɗa labarai ta France24 ta bayyana cewa za a fara kai shi birnin Paris, sannan daga nan zuwa birnin Beirut na kasar Lebanon.


 “Mun yi matukar farin ciki. Ban yi tsammanin kotun Faransa za ta taba yanke irin wannan hukunci ba, musamman bayan daƙile yunkurin sakin shi da ya nema a lokuta mabanbanta,” in ji ɗan uwansa Robert Abdallah. “A wannan karon, hukumomin Faransa kawar da ido daga matsin lamba daga Isra’ila da Amurka.” dake hana a saki a lokutan baya.


Lauyan Georges Abdallah, Jean-Louis Chalanset, ya bayyana hukuncin a matsayin “nasarar shari’a” amma kuma “abun kunya a siyasa” saboda kin sakin sa da wuri.

A wata hira da layyan ya yi da tashar Al Mayadeen, Chalanset ya ce gwamnatin Amurka ta dade tana tsoma baki wajen hana sakin Abdallah, ta hanyar matsin lamba a kan shari’ar.

Rahotanni daga wakilin kafar yaɗa labarai ta Al Mayadeen na birnin Paris ya ce hukumomin Faransa sun fara shirye-shiryen jigilar Abdallah zuwa filin jirgin sama don komawarsa gida Lebanon.

Ya kamata a saki Georges Abdallah tun shekarar 1999, amma sau 10 ana ƙin amincewa da bukatar sakin na shi. A shekarar 2013 dai an amince da ɗaya daga ciki, amma ba a aiwatar da ita ba saboda matsin lambar siyasa daga ƙasashen waje.

A wannan shekarar, wata kotun Faransa ta jinkirta sauraron karar bukatar sakin shi a karo na 11, wanda hakan ya fusata iyalan shi. A wancan lokaci, ɗan uwansa ya zargi gwamnati da ƙoƙarin "kashe ruhin gwagwarmaya" ta hanyar cigaba da tsare shi.

An kama Georges Abdallah a shekarar 1982, sannan aka yanke ma shi hukuncin daurin rai da rai a shekarar 1987 kan zargin hannu a kashe sojin Amurka Charles Ray da Jakadan Isra’ila Yakov Barsimentov da aka yi a birnin Paris. Haka kuma, an zarge shi da yunkurin kashe jakadan Amurka Robert Homme a birnin Strasbourg.

Ƙungiyar "Lebanese Armed Revolutionary Factions" (LARF) ce ta dauki alhakin aikata waɗannan kashe kashe, shi kuma Abdallah ya kasance memban wannan ƙungiya ta ƙasar Lebanon bisa wannan ne aka yanke mashi hukuncin ɗaurin rai da rai. Hakanan kuma, yana da dangantaka da Kungiyar gwagwarmayar neman ƴancin Palasɗinawa ta "Popular Front for the Liberation of Palestine" (PFLP).

Post a Comment

Previous Post Next Post