Offline

Hannun Ƙasashen Yamma Wajen Tarwatsa Gabas Ta Tsakiya A Jiya Da Yau (01):

 



Yadda Aka Rusa Daular Usmaniyya Aka Mallake Kasashen Musulmi Da Taimakon Shugabannin Larabawa

Daga Ɓangaren Palasɗinu - Palasɗinu ta kasance karkashin Daular Usmaniyya (Othman Empire) daga 1516 zuwa 1917)

Daular Usmaniyya ke gudanarwa a wannan yanki, mafi yawan al'ummar Palasɗinu a wancan lokaci musulmi ne larabawa, sai kiristoci larabawa, da kuma wani adadi mafi ƙaranci Yahudawa ne.

Wakilan daukar Usmaniyya su ke shugabanci a wannan yanki, su kuma su zabi wakilai daga cikin al'ummar ta Palasɗinu a haka ake zaune a wannan yanki, ƙasa kuwa mallakin al'ummar dake rayuwa a yankin ce mafi yawanci larabawa.

A daidai wannan lokacin kuma wannan daular tana fuskantar rigingimun cikin gida a lokaci guda kuma turawan Yamma na ta ƙoƙarin karya daular inda daga ƙarshe suka yi nasara da taimakon shugabannin ƙasashen Larabawa.

Daga cikin abubuwan da suka sabbaba ma daular Usmaniyya matsala shine ƙawance da ta ƙulla da Germany wanda ya shigar da ita yaƙin duniya a lokacin, daga cikin dalilan daular na shiga wannan ƙawance akwai:

- Domin ƙwato iyakokin daular musamman waɗanda Burtaniya, da Rasha suka ƙwace.

- Tunkude mamayar ƴan mulkin mallaka

- Zamanantar da sojojin daular bisa taimakon Germany

Wannan yasa suka ƙulla ƙawance da Germany a sirrance a ranar 2 ga watan August na shekarar 1914.

Wannan ya tsunduma su cikin yaƙin duniya a ɓangaren Germany, domin kuwa a watan Oktoban wannan shekarar ta 1914 daular ta yi amfani da jirgin ruwa na yaƙi mallakin Germany ƙirar Goeben da Breslau ta hari tashar jirgin ruwan Rasha a Black Sea.

Hakanan kuma sun yi artabu wajen korar mamayar Burtaniya da Faransa a shekarar 1915 zuwa 1916 wanda ake kira Gallipoli Campaign.

Bisa wannan ne Burtaniya ta haɗa kai da shugabannin Larabawa domin ta murƙushe wannan daula ta Usmaniyya.

Burtaniya ta haɗa baki da Shugaban Larabawan da suka yi ma daular tawaye Sharif Husaini na Makka alƙawarin za su baiwa Larabawa ƴancin kan su amma bisa sharaɗin za su taimaka ma Turawa su rusa daular ta Usmaniyya.

An yi musayar wasiƙar sirri ta ƙulla wannan kitimurmurar  tsakanin Sharif Husaini da babban kwamishinan Burtaniya na Egypt mai suna Sir Henry McMahon.

Daga cikin alƙawaruran da aka yi ma larabawa shine cewa bayan yaƙi za a basu yancin kan larabawa baki daya ciki harda Palasɗinu.

Sai dai a lokaci guda kuma Burtaniya ta zagaya ta ƙulla wata yarjejeniyar sirri da ake  kira  "Sykes–Picot Agreement" a wannan shekara ta  1916 tsakanin ta da Faransa  wannan yarjejeniya ce ta yadda za su kasa wannan yaƙi a tsakanin su.

Inda suka yarda a tsakanin su cewa :

- Za a mallaka ma Faransa wuraren da a yanzu su ne Syria da Lebanon inda suka kira "Blue Zone"

- Ita kuwa Burtaniya zata mallake wuraren da a yanzu su ne Iraq, Jordan da wasu yankunan  Palasɗinu da Turkiyya inda suka kira "Red Zone"


Bisa wannan suka haɗu suka murƙushe daular Usmaniyya tare da Larabawa musulmi daga ƙarshe kuma suka ci amanar Larabawan kamar yadda suka tsara a sirrance, bayan juyin juya halin da ake samu a Rasha a shekarar 1917 Bolsheviks ya bankaɗo takardun waccan yarjejeniyar ta Sykes–Picot Agreement (1916) ya wallafa su, anan ne shugabannin Larabawa suka gane an ci amanar su, tun daga wannan lokacin aka samu rashin jituwa tsakanin Larabawa da Burtaniya.

Bayan haka ne aka garzaya aka yi "San Remo Conference" a ranar 19 zuwa 26 na watan Afrilu na  shekarar 1920 a birnin San Remo na kasar Italiya, inda manyan kasashen da suka yi nasara a yaƙin suka yanke yadda zasu kacaccala iyakokin daular ta Usmaniyya da suka rusa a 1919, suka damƙama Burtaniya da Faransa kamar yadda suka tsara a Sykes–Picot Agreement.

Wadanda suka halarci wannan Conference sun haɗa da :

Firaministan Burtaniya: David Lloyd George

Firaministan Faransa: Alexandre Millerand

Firaministan Italiya: Francesco Nitti.

Sai kuma Jakadan Japan a matsayin mai saka ido Keishiro Matsui.

Tun daga wannan lokaci ne Burtaniya ta samu ikon mulkar Palasɗinawa a matsayin ƴar mulkin mallaka.

Zamu ci gaba akan yadda Burtaniya ta baiwa Sahayuniyawa mazauni a Palasɗinu (Yadda Yahudawa Suka Samu Mazauni A Ƙasar Palasɗinu)

©️ Mahadi Tukur Almizan - ABS Radio

Post a Comment

Previous Post Next Post