An kai harin ta'addancin ne yau juma'a akan titin Kash - Iranshahr a garin Sistan dake gundumar Baluchestan.
A bayanin da rundunar ƴan sandan yankin suka fitar sun bayyana cewa wasu gungun mutane ɗauke da muggan makamai ne suka buɗe ma jami'an tsaron na Iran wuta inda suka kashe jami'ai biyar nan take kafin su gudu.
Tweet #https
Jim kaɗan da faruwar lamarin ƙungiyar ƴan ta'adda da ake kira Jaish al-Adl ta sanar cewa ita ce ta kai wannan hari.
Jami'an tsaron Iran sun bada komar su wajen kama waɗanda suka aikata wannan aika aika.
Waɗanda aka kashe sune Kaftin Gholamreza Vahdani, da jami'an ƴan sanda uku Mohammadreza Rahimi, Mohammad Noruzi, Hassan Tavala da kuma wani jami'in soji ɗaya mai suna Hadi Royaie.
Wannan dai ba shi bane karon farko da waɗannan ƴan ta'adda suka kai hari a Iran ba musamman a garin na Sistany da gundumar Baluchestan ma baki ɗaya.
Ko a makon da ya gabata dai sun kai a Iranshahr wanda ya yi sanadiyar shahadar jami'in ɗan sanda ɗaya.
©️ Mahadi Tukur Almizan - ABS Radio
Tags
Iran
