Da Asubahin jiya Talata mazaun unguwar Mantau dake ƙaramar hukumar Malumfashi sun tsinci kan su cikin tashin hankali a daidai lokacin da suke tsaka da Sallar Asuba.
Mahara ɗauke da muggan makamai ne suka afka unguwar, suka buɗe wa masallata wuta, inda suka kashe mutum 28 kamar yadda ɗan ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe ya bayyana wa manema labarai.
Daga cikin mutanen akwai waɗanda har gidajen su maharan suka bi, suka kashe, akwai wanda ya bayyana wa manema labarai cewa har gida maharan suka je suka samu mahaifin shi, suka saka shi a ɗaki suka kulle sannan suka zuba ma ɗakin fetur suka cinna wuta ya ƙone da ran shi.
Wani daga cikin mutanen unguwar ya tabbatar ma kafar yaɗa labarai ta BBC cewa daga cikin waɗanda maharan suka ƙona da ran su akwai mata da ƙananan Yara, sannan kuma sun yi garkuwa da kusan mutum 100.
Shi ma ɗan majalisa mai wakilta Malumfashi Aminu Ibrahim ya bayyana cewa an kashe kusan mutum 30 tare da ƙona mutum 20 da ran su kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya wallafa.
Hakanan wata ma'aikaciyar asibitin General Hospital Malumfashi mai suna Fatima Abubakar ta bayyana ma kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa sun yi ma gawa 28 rijista a wurin ajiyar gawarwaki na asibitin kafin daga bisani wasu su dauki ƴan uwan su domin yi ma su jana'iza kamar yadda addinin Muslunci ya tana da.
Sai dai rundunar ƴan sandan jihar ta Katsina ta musan ta adadin da mutanen kauyen suka faɗi na waɗanda aka kashe masu.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar mai suna DSP Abubakar Sadik ya bayyana cewa mutum 15 ne suka mutu, bakwai suka samu raunuka.
Rundunar ƴan sandan ta musanta adadin da mutanen kauyen suka bayar duk da cewa sun tabbatar sun yi jana'izar mutum 28 da kan su.
Duk da haka dai kakakin rundunar ƴan sandan ya bayyana cewa ba su kama ko mutum daya daga cikin maharan ba zuwa lokacin da manema labarai suka zanta da shi amma dai ya ce sun ɗauki wasu matakan samar da natsuwa a yankin.
©️ Mahadi Tukur Almizan - ABS Radio | Matsalar Tsaro A Najeriya
Ma su karatu yaya ku ke kallon wannan lamari ?
