Offline

Amurka Ta Soke Bizar Wakilan Gwamnatin Palasɗinawa A Ƙoƙarin Hana Su Zuwa Taron Baiɗaya Na Majalisar Ɗinkin Duniya

 


- Mahadi Tukur Almizan - ABS Radio


A jiya juma'a sakataren Amurka Marco Rubio ya sanar da soke Bizar jami'an gwamnatin Palasɗinawa "Palestinian Authority" da za su halarci taron baiɗaya na majalisar ɗinkin duniya a birnin New York a cikin watan Satumba da zai shiga.


Masana na ganin wannan mataki a matsayin ƙoƙarin daƙile Yunƙurin da wa su ƙasashen Turai ke yi na amincewa da ƙasar Palasɗinu a zaman da majalisar za ta yi.


Wannan mataki da Amurka ta ɗauka saɓa ma yarjejeniyar hedikwatar majalisar ɗinkin duniya ce ta shekarar 1947, wadda ta lamunce ma duk wakilan ƙasashen majalisar ɗinkin duniya amincin zuwa ɗakin taron baiɗayan dake birnin New York ba tare da tsangwama ba.


Yarjejeniyar hedikwatar ta 1947 ta gindaya ma Amurka ƙa'idar cewa dole ta baiwa duk wakilai, ma'aikata da ƙwararru daga ƙasashen majalisar ɗinkin duniya ba tare da la'akari da alaƙar siyasar Amurka da su ba.


Mai baiwa ministan harkokin wajen gwamnatin Palasɗinu (PA) shawara kan harkokin siyasa Ahmed al-Deek ya yi Allah wadai da wannan mataki na Amurka a jiya juma'a.


Al-Deek ya yi sakataren majalisar ɗinkin duniya Antonio Gutteres da sauran mambobin majalisar su ɗauki matakin shawo kan wannan lamari da ya kira "Taka yarjejeniyar majalisar ".


Duk da cewa Palasɗinu ba mamba ba ce a majalisar amma tana daga cikin "Non-member observer" tun daga shekarar 2012 wanda ya bata damar tsoma baki a cikin tattaunawar zauren amma ba ta da hurumin jefa ƙuri'a.


Ana kallon wannan mataki da Amurka ta ɗauka a matsayin taimakon Isra'ila wajen tsira daga ta'addancin da take yi kan al'ummar Palasɗinu, tare da toshe duk wata dama da zata iya baiwa Palasɗinawa damar samun ƴantacciyar ƙasa.


Domin kuwa wannan mataki yazo ne bayan sakataren na Amurka Marco Rubio ya gana da ministan harkokin wajen haramtacciyar ƙasar Isra'ila mai suna Gideon Saar a ranar Alhamis a birnin Washington na ƙasar Amurka.


©️ ABS Radio - Al'amarin Palasɗin

Post a Comment

Previous Post Next Post