- Mahadi Tukur Almizan | ABS Radio
Tun ranar Laraba 27 ga watan Nuwamban shekarar 2024 yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Lebanon da Isra'ila ta fara aiki, wannan yarjejeniya wadda Amurka da Faransa suka shiga tsakani ta zama kamar baiwa Isra'ila damar ci gaba da kashe mutane tare da ɓarnata dukiyoyin al'ummar Lebanon cikin kwanciyar hankali domin kuwa a lokacin da ake gwabzawa tsakanin Hezbollah da Isra'ilar kowa ya san irin tashin hankalin da Isra'ila ke ciki, amma yanzu tun da ana cikin yarjejeniya Hezbollah ta daina kaima Isra'ila hare hare.
— Quds News Network (@QudsNen) September 28, 2024
BREAKING:
— Megatron (@Megatron_ron) November 24, 2024
🇮🇱🇱🇧 Hezbollah targeted Tel Aviv and Haifa, multiple impacts recorded and there are reports of casualties in neighborhoods. pic.twitter.com/GjDWJivhFf
An cimma wannan yarjejeniya ne bayan an gwabza yaƙi na tsawon kwanaki 66 tsakanin Hezbollah da Isra'ila, abinda ya jawo wanan yaƙi kuwa shi ne ta'addancin da Isra'ila take yi akan al'ummar Gaza tun bayan 07 Oktoban shekarar 2023, rundunar Hezbollah ta sha alwashin goyon bayan Palasɗinu ta hanyar kai ma Isra'ila hari domin tursasa ma Isra'ila daina harar Palasɗinawa tare da rage ma Palasɗinawan raɗaɗin hare haren Isra'ilar.
"We renew our commitment to continue the fight against the enemy, to support Gaza and Palestine, and to defend Lebanon and its resilient and honorable people."
— Quds News Network (@QudsNen) September 28, 2024
Hezbollah has confirmed the death of its Secretary-General, Hassan Nasrallah, following an Israeli attack on the… pic.twitter.com/Zu8WIDoWV0
Sakamakon haka ne ita ma Isra'ila ta riƙa kai hare hare Lebanon da sunan tana yaƙar Hezbollah, daga cikin munanan hare haren da Isra'ila ta kai Lebanon a lokacin yaƙin akwai harin da suka kai inda suka kashe sakatare janar na ƙungiyar ta Hezbollah Sayyid Hasan Nasrallah da kuma harin Pagers inda Isra'ila ta kai hari ta hanyar tarwatsa na'urorin sadarwa irin su Pagers, da Walkie Talkies na dakarun Hezbollah, wannan hari ya yi sanadiyar shahadar mutane aƙalla 40 tare da raunata aƙalla mutum dubu 3.
— Matt murdock🚀 (@mattmurock123) September 17, 2024
Hacking possibilities of phones #Hezbollah guys using #Pagers only.#Israel tapped the pagers distribution network in Lebanon and injected malware into all devices.#Mossad exploded all pagers owned By Hezbollah .
pic.twitter.com/k5Y7cH2R1M
Tun bayan ƙulla yarjejeniyar tsagaita wutar ta watan Nuwamban 2024 Haramtacciyar ƙasar Isra'ila ta cigaba da kai hare haren ta'addaci kudancin ƙasar Lebanon, a wani rahoto da wakilin kafar yaɗa labarai ta Almanar mai suna Ali Shu'aib ya fitar ya bayyana yadda sojojin haramtacciyar ƙasar ta Isra'ila ke karya ka'idojin da aka gindaya ciki har da yin kutse cikin iyakokin ƙasar ta Lebanon duk da cewa yana daga cikin sharuɗɗan yarjejeniyar cewa Isra'ila zata janye dakarun ta daga iyakokin Lebanon, wakilin na Almanar ya bayyana yadda ya ga sojojin Isra'ila aƙalla 20 su na rangadi a kusa da gaɓar kogin Wazzani (Wazzani River).
Ali Shu'aib ya labarto yadda sojojin na Isra'ila suka kutsa cikin garin Mais Al-Jabal har suka yi tafiyar mitoci 500 zuwa kusa da asibitin garin.
Ya ƙara da cewa "Dakarun maƙiya sun afka cikin wani kamfani duk da cewa sun lalata komai dake cikin wannan kamfani tun wancan lokacin da aka yi yaƙin na kwanaki 66 a shekarar da ta gabata ta 2024, mai kamfanin ne ya sake ginawa a ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arzikin yankin bayan ta'addancin Isra'ila.
Ta'addacin Isra'ila ba a iya rushe rushen gine gine da ɓarnar dukiya kawai ya tsaya ba, har da kashe rayuka domin ko a jiya juma'a sun kai munanan hare hare garin Ayta Al-Shaab inda suka buɗe wuta a wani gida kamar yadda kafar yaɗa labarai ta Almanar ta tabbatar.
Hakanan shekaran jiya Alhamis sojin Isra'ila sun harba drone inda yaje ya hari wata motar fararen hula a unguwar Khalde dake kudancin birnin Beirut inda aka samu shahidi 1 tare da masu raunuka 3, hakanan kuma sojin na Isra'ila sun hari garuruwan bayan gari a kudancin na Lebanon wannan kuma ya saɓa da Resolution 1701 na majalisar ɗinkin duniya.
Wasu alƙaluma sun nuna cewa daga 27 November 2024 zuwa yau Isra'ila ta keta yarjejeniyar ta hanyar kai hare hare har sama da 3,500.
- A ranar 11 ga watan Janairun wannan shekarar da muke ciki ta 2025 alƙaluman kafafen yaɗa labaran Lebanon sun nuna cewa an samu keta yarjejeniyar sau 455 daga 27 November.
- Daga 31 January 2025 adadin ya haura zuwa 823.
- Zuwa yau ana ƙiyasta adadin keta yarjejeniyar zuwa 3505.
#Hezbollah #Israel #FreePalestine #HezbollahIsrael66DaysWar #Ceasefire
