Daga Bin Muhammad
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya musanta kalaman shugaban Amurka dangane da muradin Iran na gudanar da tattaunawa, yana mai jaddada cewa: A bangaren Iran ba a gabatar da wata bukata ta yin wata ganawa da bangaren Amurka ba.
Da yake mayar da martani ga kalaman Donald Trump, Ismail Baqa’i ya ce: Iran tana musanta abin da Trump ya fada game da bukatar Iran na gudanar da tattaunawa, kuma ba ta gabatar da wata bukata ta ganawa da Amurkawa ba.
Yayin ganawarsa da Fira ministan gwamnatin Isra’ila Benjamin Netanyahu da yammacin ranar Litinin, Trump ya yi ikirarin cewa an sanya ranar tattaunawa da Iran, yana mai cewa: Iraniyawa suna son tattaunawa da Amurka.
A wani bangare na jawabin nasa, Trump ya sake nanata ikirarinsa game da shirin makamashin nukiliyar Iran, yana mai cewa: Ya yi imani cewa Iraniyawa suna son ganawa da Amurka ne domin samun zaman lafiya, ya kara da cewa; An lalata shirin makamashin nukiliyar Iran gaba daya, kuma hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta tabbatar da cewa an lalata wurin da Amurka ta kai hari a Iran.
