Offline

Gangamin Goyon Bayan Al'ummar Palasɗinu A Faɗin Ƙasar Yemen A Yau Juma'a



 - Mahadi Tukur Almizan | ABS Radio 

Al'ummar Yemen sun sake fitowa a yau juma'a domin sake jaddada goyon bayan su ga raunana Palasɗinawa da Isra'ila ke kashewa dare da rana.


A yau al'ummar gundumar mulki ta birnin Sa'ada, Raymah da kuma birnin Ma'arib sun gudanar da gagarumin gangamin nuna goyon bayan al'ummar Palasɗinu tare da nuna rashin amincewa da ta'addacin Isra'ila akan a'ummnar Palasɗinu.




Masu gangamin sun fito ƙwai da ƙwarƙwata suna ɗaga sauti suna rera taken jaddada goyon bayansu ga Palasɗinu tare da tofin Alatsine kan Isra'ila musamman a ta'addancin da take cigaba da yi a zirin Gaza.


Al'ummar Yemen dai su ne aka sani da nuna goyon baya ga Palasɗinu daga al'ummar ƙasar har zuwa hukumomi n ƙasar, domin kuwa ko a ƴan kwanakin nan Shugaban ƙungiyar Ansarallah Sayyid Abdulmalik ya jaddada matsayar su na cigaba da hana jiragen dakon kayan Isra'ila wuce wa ta mashigar Bab Almandab.

#Yemen #Ansarallah #Houthi #FreePalestine

Post a Comment

Previous Post Next Post