Daga-Bin Muhammad KD
Tashar talabijin din “Cane” ta HKI ta bukaci Amurka da ta kafa kawance mai fadi na kasashe domin fuskantar kasar Yemen.
A yayin ziyarar da Fira ministan HKI, Benjamin Netanyahu a Amurka ne dai ya bijiro da wannan bukatar, kamar yadda rahoton tashar talabijin din ta “Cane” ya ambata.
Rahoton ya kuma ce, Jami’an HKI sun sanar da Amurka cewa, ci gaba da hare-haren Yemen, ya tashi daga zama matsalarta ita kadai, don haka da akwai bukatar kai hare-hare na hadin gwiwa da Amurka da kuma shigar da kasashen wannan yankin da kuma wasu na duniya.”
Tun daga 2023 dakarun Ansarullah na Yemen ke kai wa jiragen ruwa na HKI hare-hare a cikin tekun “Red Sea” ko kuma wadanda su ka nufi tasoshinta na jirgin ruwa. Sojojin na Yemen dai sun sha bayyana cewa ba za su daina kai hare-haren ba har sai an kawo karshen yakin Gaza, da kuma dauke takunkuman da aka kakabawa yankin.
Shugaban kungiyar Ansarullah ta Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husi ya sha bayyana matsayar kasar ta Yemen yana mai cewa; Hare-haren nasu martani ne akan laifukan yakin da HKI take yi a Gaza, ba kuma za su daina ba, sai an dakatar da aikata wadannan laifukan.
