Offline

"ECI" ta Ƙaryata Iƙirarin Ishaq Herzoq Na Karɓar Baƙuncin Limamai Daga Turai.



Daga- Bin Muhammad KD 

Majalisar limaman musulmin nahiyar turai da ake kira "European Council of Imams" ta fitar da wani bayani inda ta nesanta kanta daga wasu mutane da su ka kai ziyarar haramtacciyar ƙasar Isra'ila tare da bayyana kansu a matsayin limamai daga kasashen turai, tana mai cewa, ko kadan ba su wakiltar al’ummar musulmin da suke cikin nahiyar ta turai.

A ranar Litinin din da ta gabata ne dai ofishin shugaban haramtacciyar ƙasar Isra'ila wato President Ishaq Herzog ya fitar da bayani da a ciki yake cewa; A ofis dinsa dake birnin Kudus ya karbi bakuncin limaman musulmi daga kasashen Faransa,Belgium, Holland, Italia da kuma Birtyaniya.”.

Ofishin majalisar limaman musulmin na turai, mai  matsugunni  a Faransa ya bayyana ziyarar mutanen zuwa Isra’ila da cewa, tana da daure kai, haka nan kuma lokacin da aka yi ta.”

Majalisar ta limaman turai din ta yi kira ga dukkanin ‘yantattu a duniya da su kasance a tare da al’ummar Falasdinu da ake zalunta, domin ganin an kawo karshen kisan kiyashin da sojojin mamaya suke yi musu.

Bugu da kari majalisar ta ce, wannan ziyarar tana nuni da yadda wadanda su ka yi ta ba su da lamiri na ‘yan’adamtaka da rashin riko da mafi karancin koyarwar musulunci ta yin kira da a taimaki gaskiya.”


Majalisar limaman na Turai ta kuma kara da cewa; ziyarar wani kokari ne na wanke ‘yan mamaya, kuma cin amanar Allah da manzon Allah ne da jinanen raunana.

Post a Comment

Previous Post Next Post