Daga-Bin Muhammad KD
Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh ya bayyana cewa: Munanan hare-haren da sojojin kasar Iran suka kaddamar a matsayin mayar da martani ga yahudawan sahayoniyya ne suka kai ga neman tsagaita bude wuta.
A wata tattaunawa ta wayar tarho guda biyu da ya yi da ministocin tsaron Venezuela da Armeniya, Birgediya Janar Nasirzadeh na rundunar sojin sama ya jaddada cewa: Hare-haren da sojojin Iran suka kaddamar kan yahudawan sahayoniyya ne suka kai ga neman tsagaita wuta.
Ministan tsaron na Iran ya kara da cewa: Sojojin kasar Iran sun shirya tsaf domin mayar da martani ga duk wani yunkuri ko wauta daga ‘yan sahayoniyya da masu mara musu baya a cikin yanayi mai raɗaɗi da nadama.
Ya ci gaba da cewa: Hare-haren da yahudawan sahayoniyya suka kai a lokacin tattaunawa da Amurka wani karin shaida ne na rashin dogaro da Amurka da kasashen yamma.
