Daga-Bin Muhammad KD
Shugaban yahudawan Iran Rabbi Younes Hamami Lalezar ya ce, Isra’ila tana amfani da addinin yahudanci domin cimma manufofinta, tana kuma bayyana Iran a matsayin wacce take fada da addinin yahudanci,alhali a cikin Iran da akwai zaman lafiya tsakanin Mabiya dukkanin addinai.
Haka nan kuma ya ce, kiyayyar da Isra’ila take da shi akan Iran ne, yake sa take jingina wa Iran din kin jinin yahduawa,wanda aikin ‘yan sahayoniya ne su samar da rabuwar kawuna a tsakanin al’ummar Iran bisa addini da kuma kabila.
Isra’ila tana bayyana kanta a matsayin mai bai wa yahudawa kariya, sai dai da dama daga cikin Mabiya addinin yahudanci, wadanda ba ‘yan sahayoniya ba, suna zarginta da amfani da addini saboda manufofi na siyasa.
Fiye da shekaru 2,700, yahudawa suke rayuwa a cikin Iran,kuma suna da wuraren bautarsu da harkokinsu na yau da kullum ba tare da tsangwama ba.
Rabbi Younes Hamami Lalezar ya kuma ce: A Iran, yahudawa suna aiki, suna yin bautarsu, da rayuwa a ko’ina, suna da dakunansu na ibada -Synagogues- a cikin sauki da ‘yanci ba tare da wata kariya ta jami’an tsaro kamar yadda yake a cikin kasashen turai ba.
Haka nan kuma ya ce, yadda muke rayuwa ta girmama juna a tsakanin musulmi, yahudawa, da kiristoci, shi ne babban abinda yake bayyana hakikaninmu, don haka duk wani zargi na kin jinin yahudawa ba shi da madogara.”
