Daga - Mahadi Tukur Almizan & Nusaiba Atiku
Tun yana da ƙananan shekaru, Abu shujaa ya shiga gwagwarmayar neman ƴanci daga mamayar Isra'ila, wanda ya yi sanadin kama shi karon farko yana ɗan shekara 17.
Sojin Isra'ila sun shelanta cewa sun kashe Mohammed Jaber Abu shujaa , tare da wasu membobi hudu cikin na Bataliyar shi, a ranar wata Alhamis da sojin na Isra'ila suka da wani mummunan hari a sansanin 'yan gudun hijira na Nur Shams a Tulkarm.
Jaber, wadda aka fi sani da sunan shi na filin daga Abu Shujaa, ya kasance mutum mai muhimmanci kuma kwamandan rundunar Tulkarm (Tulkarem Battalion) mai alaƙa da Al-quds Brigade , ɓangaren soji na ƙungiyar Palestinian Islamic Jihad Movement.
Abu shujaa ya kasance daya daga cikin wadan suka samar da wannan rundunar ta Tulkarem Battalion tare da kwamandan ta na farko, Saif Abu libdeh
Haihuwar shi Da Tushen shi
An haifi Abu Shujaaa a shekarar 1998 a sansanin Nur Shams, wanda yake a Tulkarm dangin sa asalinsu daga Haifa ne, an rabasu da muhallin su a alokacin Nakbar shekarar 1948. Ya taso a sansani, kuma shine ɗa na tsakiya acikin su biyar.
Abu shujaa yayi makaranta a sansanin Nur Shams Amma matsin rayuwa ya tilasta ma shi barin makaranta.
Da ƙananan shekaru, Abu shujaa ya tsunduma yakin neman ƴanci daga mamayar haramtacciyar ƙasar Isra'ila, wanda ya yi sanadin kamun a karon farko yana ɗan shekara 17.
Daga baya an kamashi har sau biyu. Yayi kusan shekaru 5 a gidan yarin Isra'ila, hakanan kuma hukumomin tsaro na gwamnatin su Mahmoud Abbas (Palestinian Authority) sun tsare shi har sau biyu.
Rundunar Tulkarm (Tulkarem Battalion)
A watan March na shekarar 2022, Abu shujaa tare da wanda ya zama kwamandan rundunar na farko mai suna Saif Abu labdeh, da kuma wasu matasa daga sansanin Tulkarm da Ain Shams suka haɗu suka samar da wannan runduna.
Bayan an kashe kwamanda Abu Labdeh a ranar biyu ga watan April a wannan shekarar ta 202, Abu shujaa ya karɓi kwamandancin rundunar. A karkashin jagoranci sa rundunar ta bunƙasa inda ta karu da mayaƙa wajen 40 daga April zuwa September na shekarar ta 2022.
Rundunar ta Tulkarm dake da Alaka da Al-quds Brigade ta ƙunshi mayaƙa daga wasu ƙungiyoyin gwagwarmayar Palasɗinu mabanbanta. A watan February na shekarar 2023 suka haɗe da gungun dakarun martanin gaggawa da aka fi sani da "Rapid Response Group"wannan wani gungun mayaƙa ne da mayaƙi Amir Abu Khadija ya samar a ƙarƙashin rundunar Al-Aqsa Matyrs Brigade ta ƙungiyar Fatah Movement.
Rundunar ta ci gaba da ƙarfafa haɗin gwuiwa mai ƙarfi tsakanin ta da sauran kungiyoyin gwagwarmaya da ke Nablus, Jenin, da wasun su.
Duk da an kafa rundunar ta Tulkarem Battalion ne a sansanin Nur Shams amma suna gudanar da ayyuka a faɗin Yammacin Gabar Kogin Jordan (West Bank), inda suke kai farmaki kan sojojin Isra'ila a shingayen bincike tare da hana kutsen makiya cikin sansanonin dake Tulkarm da Nur Shams. Rundunar ta yi kokarin inganta ayyukan ta koyar da dabarun yaƙi, kera abubuwan fashewa, da kuma kafa sashen jigilar kayan aiki.
Yunƙurin Hallaka Kwamanda Abu Shujaa.
Sojojin mamaya na Isra'ila sun ayyana Abu shujaa a matsayin babbar barazana a arewacin yammacin gabar kogin Jordan (Nothern west bank).
Sojojin haramtacciyar ƙasar Isra'ila sun yi ta yunƙurin kashe shi a lokuta mabanbanta, hakanan su ma jami'an hukumomin tsaron gwamnatin su Mahmoud Abbas (Palestinian Authority) dake mulkar yammacin gaɓar kogin Jordan sun yi ta neman rayuwar shi a lokuta mabanbanta.
Tsakanin watan April da May na shekarar 2024, dakarun gwamnatin Palestinian Authority ta su Mahmoud Abbas ta kashe mayaƙa biyu Khaled Al-Aref da Ahmad Abu Al-Foul na rundunar Abu Shujaa.
Har Dangin Abu Shujaa basu tsira daga yunkurin kisa ba:
An kashe ɗan uwan shi mai suna Mahmud a wani lokaci da sojin Isra'ila suka yi ma Sansanin Nur Shams ƙawanya, hakanan kuma an sha kama babban ɗan uwan shi mai suna Oday, tare da kanin sa Ahmad.
Sojojin mamaya na Isra'ila sun ruguza gidan su, hakan ta sanya dole su nemi mafaka a gidajen makofta duk lokacin da suka kawo hari.
Labaran Ƙarya Akan Shahadar Shi:
A watan ranar 19 ga watan April na shekarar 2024 , sojojin Isra'ila suka shelanta cewa sun kashe Abu shujaa a wani hari da suka kai wani gida a cikin sansanin Nur Shams, inda suka ce wai ya ɓuya tare da wasu mayaƙa .
Wannan hari haɗaka ne tsakanin jami'an tsaron cikin gida na Isra'ila, Shabak da jami'an kula da iyakar haramtacciyar ƙasa, inda aka tafka mummunan gumurzu.
Bayan fitar wannan rahoto ne mahaifin shi da ƴan uwan shi suka tabbatar da shahadar har ma suka fara zaman karɓar ta'aziyya a masallaci a gefe guda kuma rundunar shi ta ƙaryata labarin shahadar ta shi
Bayan kwanaki biyu kwatsam sai Abu shujaa ya bayyana abainar jama'a, yana rike da bindigarsa a wajen jana'izar abokan aikin shi da suka yi shahada a Tulkarem, anan ya faɗi wasu kalmomi yana ƙalubalantar iƙirarin Isra'ila na kashe shi.
🚨#BREAKING
— Middle East Observer (@MiddleEObserver) April 21, 2024
Earlier, reports said that the commander of Tulkaram Battlion in Saraya Al-Quds “Abu Shujaa” was martyred by zionist terrorists.
Today, #AbuShujaa surprised them and appeared at a funeral for martyrs, and it turned out that the Israelis weren’t able to kill him! pic.twitter.com/YaTpykfW2K
"Saƙon mu ga ƴan mamaya shine bamu sare ba, muna nan bisa tafarkin Shahidai, gwagwarmayar mu zata ci gaba har zuwa ga nasara" ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a muhallin jana'izar shahidan, a lokaci guda kuma ya miƙa sakon jinjina ga al'ummar Palasɗinu bisa goyon bayan ƴan gwagwarmaya.
Soyayyar Da Al'ummar Sansanin Suke Yi Ma Shi Tasa Suke Bashi Kariya:
A ranar 26 ga watan July na shekarar 2024 dandazon al'ummar Tulkarem suka bashi kariya daga yunƙurin dakarun hukumar "Palestinian Authority" a lokacin da suka yi yunkurin kama shi a asibitin Thabet Thabet Hospital a daidai lokacin da yazo asibitin ana yi mashi maganin wani ciwo da yaji a lokacin da wasu abubuwa suka fashe suna ƙoƙarin haɗa Bom.
A daidai wannan lokacin ne labari ya karaɗe ko ina cewa jami'an Palestinian Authority sun zagaye su Abu Shujaa a asibitin nan take bangarorin gwagwarmaya suka shelanta gangami domin ƴan to su Abu Shujaa, nan take suka hallara a asibitin aka ci gaba da musayar wuta tsakaninsu da dakarun Palestinian Authority, ƙarshe al'ummar yankin suka tsaya ƙyam suna rera taken "Rayuwar mu fansar Abu Shujaa" a haka suka ƴantar da shi daga asibitin.
ابو شجاع. ماذا حدث في مستشفى طولكرم؟
— مَحْمُودْ سَالِمْ الْجِنْدِي (@DrMahmoudSalemE) July 26, 2024
1️⃣ بعد إصابة القائد ابو شجاع ووصوله للمستشفى أجهزة السلطات تحركت إلى هناك.
🔴 تجمهر الاهالي لتأخير تقدم رجال عباس.
3️⃣ وصل رجال المقاومة..
4️⃣ والذين بمجرد وصولهم انسحب وهرب رجال عباس.
5️⃣ خرج ابو شجاع مرفوع على الأكتاف.
6️⃣ وصل لمخيم نور شمس… pic.twitter.com/KZZioaPmAE
A wata tattaunawa da yayi da kafar yaɗa labarai ta ƙasar Lebanon Almayadeen wadda suka wallafa a ranar 16 ga watan August ya isar da saƙonni zuwa ga al'ummar Gaza.
"Mun koyi jajircewa da hakuri ne daga ƴaƴa da mayaƙan Gaza, mun samu ƙwarin gwuiwa ne daga gare su".
"Gwagwarmaya ta ci gaba da nuna jarumtaka da ƙwazo a fagen yaƙi daban-daban cikin waɗannan watanni goma da fara yaƙi, duk da munanan laifuffukan yaƙi da Isra'ila ke aikatawa inda suke kai farmaki kan fararen hula, mata da yara," in ji shi, yana nuni da kisan gillar da aka yi wa fararen hula na Palasɗinu a makarantar Tabaeen a ranar 10 ga watan na August.
"Ku mutane ne masu ƙarfin hali da ƙuduri, kun tabbatar wa duniya cewa mutanen Gaza za su iya kawar da Isra'ila," a cewar Abu Shujaa, ya yi kira ga shugabannin gwagwarmaya kada su yi ƙasa a gwuiwa wajen neman ƴanci.
"Ko da maƙiya sun kashe ni, za mu cigaba," in ji shi.
ya ƙare da cewa, "Gwagwarmaya ba ta tsayawa da kawo karshen mutum guda, akwai wasu sabbin ƙarni da za su tashi su kare hakkokinmu, kuma babbar shaida ita ce shahidan Palasɗinu, akwai Shahidai kowane gida a Tulkarem da Palasɗinu baki ɗaya, dan haka gwagwarmaya zata ci gaba".
Shahadar Abu Shujaa
A ranar 29 ga watan August na shekarar 2024 Abu Shujaa ya yi shahada sakamakon wani hari da jami'an hukumar Shin Bet na "Yamam Counter Terrorism Unit" suka kai wani masallaci a Nur Shams dake wajen Tulkarem.
⚡️BREAKING:
— Suppressed News. (@SuppressedNws) August 29, 2024
The commander and founder of the Tulkarem Brigade, Abu Shujaa was killed during israel’s cowardly aggression in Nour Shams Camp, Tulkarem, West Bank. It has been reported that there are five total martyrs as a result of the invasion.
He previously survived multiple… pic.twitter.com/27109mT1fm
Amincin Allah a gare ka ranar da ka aka haifeka zuwa ranar da kayi shahada da ranar da za a tashe ka a sahun shuhada.
.jpeg)