Offline

Aƙalla Palasɗinawa 40 Isra'ila Ta Kashe A Wajen Rabon Kayan Tallafi A Yau Lahadi



 - Mahadi Tukur Almizan 

Dakarun sojin Isra'ila sun ƙaddamar da sabon kisan kiyashi akan Palasɗinawa a Gaza a yayin da suke hanyar zuwa karbo kayan tallafi wanda ake rabawa sansanin gudun hijira na Al-Mawasi dake Rafah kudancin Gaza.


Wannan mummunan lamari ya faru ne da sanyin safiyar yau Lahadi, wanda yayi sanadiyyar rayukan sama aƙalla 30 a rahoton 'The Cradle, a wani rahoton baya bayan nan da kafar yaɗa labarai ta middle east eye ta wallafa ya nuna adadin waɗanda suka rasa rayukansu ya kai Palasɗinawa 40.


Wannan hari ya raunata mutum 220 kamar yadda hukumar agajin lafiya ta Palasɗinawa "Palestinian Medical Relief Agency" ta bayyana.


Ba wannan bane karon farko da Isra'ila ta kai hari wannan muhalli na rabon kayan tallafi ba a cikin wannan mako, biyo bayan waɗannan hare hare ofishin yaɗa labarai na gwamnatin Gaza ya ayyana wannan muhalli a matsayin tarkon mutuwa a maimakon wurin samun tallafin jin ƙai.


"Waɗannan muhallai sun zama tarkon mutuwa a maimakon wurin samun tallafin jin ƙai, abinda ke faruwa wata shiryayyar dabara ce ta amfani da kayan tallafin a matsayin wani makamin yaƙar Palasɗinawa" domin an yunwatar da su sannan kuma an tattara su waje ɗaya da sunan za a raba kayan agaji amma ana kashe  su.


Hakanan da safiyar yau Lahadi ɗin sojin Isra'ila sun tarwatsa unguwar Qizan al-Najjar dake birnin Khan Yunis a kudancin zirin Gaza ta hanyar jefa bom, a lokaci guda kuma suna aikin rushe muhallan Palasɗinawa a gabashin birnin.


Jefa boma boman da Isra'ila ta yi ya kai har unguwar Al-Tuffah dake makotaka da gabashin Gaza, a lokaci guda motocin dakarun sojin na Isra'ila da jiragen yaƙi na cigaba da harar Jabal Al-Sorani dake gabashin unguwar ta Al-Tuffah.

Post a Comment

Previous Post Next Post