Jiragen yaƙin haramtacciyar ƙasar Isra'ila sun kai wani sabon hari tashar jiragen ta kasar Yemen dake birnin Sana'a a jiya Laraba 28 May, harin ya yi sanadiyyar tarwatsa jirgin kamfanin Yemenia Airways.
👉
Kafar yaɗa labaran kasar ta Yemen Al-masirah news ta bayyana cewa "Jiragen yaƙin Isra'ila 4 ne suka hari tashar jiragen ta Sana'a, inda suka tarwatsa jirgin kamfanin Yemenia Airways".
Sai dai bayan harin rediyon sojin haramtacciyar ƙasa ya bayyana cewa sun hari babbar tashar jiragen sama ta Yemen dake birnin Sana'a sannan kuma sun tarwatsa wani jirgi a tashar mallakin ƙungiyar ƴan Houthi, a cewar su wai ƴan Houthi na amfani da jirgin wajen jigilar ƴan ta'adda masu yaɗa ƙiyayyar haramtacciyar ƙasar Isra'ila.
👉
Sama da jiragen yaƙin Isra'ila 10 ne suka yi musharaka wajen kai wannan hari cewar kafar yaɗa labarai ta Isra'ila Channel 1
Idan baku manta ba dai tun a farkon wannan wata da muke ciki na May ne Isra'ila ta kaddamar da wasu mummunan hare hare uku, biyu a tashar jiragen ruwa ta Hodeidah da Salif, sai hari na ukun a tashar jiragen sama ta Sana'a ɗin da suka sake kai ma hari jiya Laraba, a sakamakon wancan harin da Isra'ila ta kai ma wannan tashar jiragen saman sai da aka kulle shi na tsawon kwanaki 10.
Tun bayan wancan hari na Isra'ila kan Yemen, su ma Yemenawa suka shiga harar tashoshin jiragen saman Isra'ila, domin kuwa ko a shekaran jiya Talata 27 May sun kai tagwayen hare hare a tashar jiragen saman Isra'ila da ake kira "Lod Airport" wadda aka fi sani da Ben Gurion Airport, sun hari wannan tasha da ballistic missile mai suna "Palestine-2" wannan missile Hypersonic ne.
Missile na biyu mai suna "Zulfiqar" ya hari wani gungun ƴan mamaya a yankin Jerusalem wato Jaffa da Isra'ila ta mamaye.
Wannan hare hare Isra'ila na zuwa ne sakamakon cigaba da ayyukan taimakon Palasɗinawa da rundunar Ansarullah ta Yemen ke ci gaba da aiwatarwa.
Sakamakon hare haren na dakarun Ansarullah na Yemen kamfanonin jiragen sama mabanbanta ne suka daina zuwa Isra'ila.
Ciki har da kamfanin Lufthansa Group da kuma kamfanin ITA na ƙasar Italiya sun dakatar da jigilar fasinjoji har zuwa ranar 8 ga watan Mayu.
Shi ma kamfanin jiragen sama na Seychelles ya dakatar da jigilar fasinjoji a watan June da July, ya tabbatar ba zai dawo aiki ba har sai August
A ranar Litinin ɗin da ta gabata shima CEO na kamfanin Ryanair mai suna Michael O'Leary ya bayyana ma manema labarai cewa "Hakurin kamfanin wajen zuwa Isra'ila da ɗauko fasinja daga Isra'ilar ya ƙare saboda rashin tsaro" ya kara da cewa idan har aka cigaba a haka to lallai kamfanin zai canza akalar harkar jigilar ta shi daga Isra'ila.
