Offline

Ramallah: Sojojin Isra'ila sun kashe wasu Palsdinawa biyu

Yan uwan ​​daya daga cikin mutanen da aka kashe, Bassel Basbous, dan shekara 18, suna yin makoki a wajen jana’izar sa a gidansu da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Jalazone a ranar Litinin, 3 ga Oktoba.



An harbe wasu matasan Falasdinawa biyu har lahira tare da raunata wata a ranar Litinin bayan da sojojin Isra'ila suka bude wuta kan wata mota kusa da Ramallah a yankin yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye, a cewar ma'aikatar lafiya ta Falasdinu.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma'aikatar ta ce an sanar da ita, game da "Shahadar 'yan kasar biyu, bayan da sojojin mamayar suka bude musu wuta a kusa da sansanin 'yan gudun hijira na Jalazone," a arewacin Ramallah.

Majiyoyin yada labarai na cikin gida sun bayyana sunayen matasan Basel Basbous da Khaled al-Dabbas, dukkansu daga sansanin Jalazone. Ita ma Salama Raafat, 'yar garin Birzeit, tana cikin motar kuma ta samu raunuka yayin harbin.

Sojojin Isra'ila sun ce "sun kashe mutane biyu da suke zargi", suna ikirarin cewa "sun yi yunkurin kai harin bam kan sojojin IDF".

sun kara da cewa sun kama mutane 16 a wani samame da suka kai cikin dare a yammacin gabar kogin Jordan da suka mamaye.

A ranar Asabar din da ta gabata ce sojojin Isra'ila suka harbe Fayez Khaled Damdum dan shekaru 18 da haihuwa a gabashin birnin Kudus da suka mamaye, a wani samame da suka kai a yankin.

Garuruwan Falasdinawa da suka mamaye na fuskantar karuwar tashe-tashen hankula a cikin 'yan makonnin da suka gabata a daidai lokacin da ake tsaurara matakan tsaro gabanin bukukuwan Yahudawa.

Dakarun Isra'ila na kai hare-hare da kame kusan kullum a sassa daban-daban na Yammacin Gabar Kogin Jordan, lamarin da yake kai wa ga jikkata ko kuma kashe Falasdinawa.

A farkon makon nan ne sojojin Isra'ila suka kashe Falasdinawa hudu tare da jikkata wasu fiye da 40 a wani samame da suka kai a birnin Jenin da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan da suka mamaye.

Fiye da Falasdinawa 150 ne Isra’ila ta kashe a wannan shekara, ciki har da 49 a Zirin Gaza da kuma akalla 100 a yankin Yamma da Kogin Jordan da ta mamaye da kuma Gabashin Kudus. Adadin wadanda suka rasa rayukansu a yammacin gabar kogin Jordan shine mafi yawa tun shekarar 2015.

Post a Comment

Previous Post Next Post