Amurka na cigaba da kasancewa mai samar da Boma-boman da Isra'ila ke amfani da su domin kawar da Palasɗinawa daga doron duniya bayan ƙasar Germany da Italy.
Jirgin Jigilar makamai ya sauke kayan makamai da ya yi dako daga Amurka zuwa Isra'ila sumul ƙalau, wannan shine karo na 800 da jirgin Amurka ya kai makamai zuwa Isra'ila, wannan jirgi a sauka a birnin Tel Aviv ne a jiya Laraba 27 May, a cewar ma'aikatar tsaron Amurka daga fara wannan yaƙi Amurka ta kai sama da ton dubu 90 na makamai da kayan sojin Isra'ila.
Isra'ila ta bayyana wannan safarar makaman da Amurka ke yi mata babu ƙaƙƙautawa ta sama da ruwa (ta hanyar amfani da jiragen sama da na ruwa) a matsayin wata babbar gudummawa da zata baiwa Isra'ila damar ƙaddamar da manufar ta na share Palasɗinawa daga doron ƙasa wanda aka shiga rana ta 600 a jiya Talata.
Eight hundred transport planes and 140 ships have delivered more than 90,000 tons of armaments and military equipment from the United States to Israel since the start of the war, the Defense Ministry says.
— Emanuel (Mannie) Fabian (@manniefabian) May 27, 2025
This morning, the 800th plane landed, according to the ministry.
The… pic.twitter.com/I0KZjWB04K
A cikin watanni sama da 19 da suka gabata Amurka ta aika ma Isra'ila da makamai da suka kai na kimanin dalar Amurka biliyan 30 ciki har da dala biliyan 7.4 na missile da boma - bomai a watan February da kuma dala biliyan 3 na ƙunshin "Emergency arms package a watan March".
A wani rahoto da jami'ar 'Brown University' ta wallafa a shekarar da ta gabata akan kuɗaɗen da Amurka ta kashe wajen yaƙe-yaƙe ya nuna cewa Amurka ta kashe aƙalla dalar Amurka biliyan $22.76 daga watan October na shekarar 2023 zuwa 30 ga watan September n shekarar 2024, wannan tallafa ma Isra'ila ne domin ta cigaba da kisan kiyashin da take yi a Gaza tare da cigaba da kunna wutar rikice rikice a gabas ta tsakiya.
Ko a watan da ya gabata majalisar dokokin Amurka ta daƙile wasu ƙudororin nuna rashin amincewa da aika ma Isra'ila taimakon soji.
Hakanan a watan March na wannan shekarar firaministan haramtacciyar ƙasar Isra'ila Benjemen Netanyahu ya shaidi Trump akan irin taimakon da yake yi masu na makamai inda ya bayyana cewa "Haƙiƙa Donald Trump babban aminin Isra'ila ne fiye da duk wani shugaban Amurka da ya gaba ce shi, ya nuna haka ta hanyar aiko mana da makaman da gwamnatin da a gabace shi ta hana mu, bisa wannan yanzu ya baiwa Isra'ila kayan aikin da ta ke bukata domin kammala aikin ganin bayan ƴan koren Iran (Ƴan Muqawama).
A halin yanzu sama da tons 100,000 na Boma-bomai ne Isra'ila ta jefa a Gaza, wanda wannan ya zarce adadin gaba ɗaya boma boman da aka jefa a Dresden da birnin Hamburg a Gomorrah Operation da kuma wanda na 'The Blitz' lokacin yaƙin duniya na 2, wanda idan aka tattara waɗannan ukun gaba ɗayan su ton 32,300 ne na boma boman da aka jefa, amma a Gaza cikin ƙasa da shekaru 2 an jefa sama da ton dubu 100.
Wani likita ɗan ƙasar Birtaniya da ya je aikin agaji a asibitin Nasser Hospital dake Khan Yunis a kudancin Gaza ya bayyana wa manema labarai cewa "Tun da nake ban taɓa ganin raunukan fashewar Bomb ba kamar yadda na gani a Gaza ba" a cewar Victoria Rose.
Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta tabbatar da Shahadar mutum 54,000 daga far wannan yaƙi da Isra'ila wanda Amurka ke ɗaukar nauyi.
A watan da ya gabata hukumomi a Gaza sun bayyana cewa kaso 65% na waɗanda Isra'ilar ta kashe mata ne da ƙananan yara da kuma tsofaffi.
Sun kara da cewa Isra'ila ta shafe iyalai sama da 2,180 a doron duniya.
