Offline

Isra'ila Ta Hari Masu Gadin Ayarin Motocin Kayan Agaji Zuwa Gaza Ta Hanyar Amfani Da Jiragen Sama

 


 - Mahadi Tukur Almizan


A cigaba da ta'addancin da Isra'ila ke yi na yunwatar da PalasÉ—inawa, tana ci gaba da taimakon masu wawushe kayan agaji a hanyar su ta shiga Gaza.

A ranar juma'a 23 May, gwamnatin Gaza ta bayyana cewa aƙalla jami'an tsaro 6 dake rakiyar ayarin motocin kayan agaji ne suka yi shahada, wannan jami'an tsaro suna aikin kare kayan agajin ne daga ƴan mamaya masu wawushe kayan agajin.

Gwamnatin ta bayyana cewa Isra'ila ta kashe wadannan masu aikin tsaron kayan agajin ne ta hanyar harbi da jiragen sama, inda ta ƙaddamar da hare hare mabanbanta da jiragen sama har sau 8 akan waɗannan bayin Allah masu aikin kare kayan agajin.

Sojin Isra'ila dai sun toshe hanyar shiga da kayan agaji zuwa zirin Gaza na tsawon makonni 11, kafin su bari a shiga da wasu ƴan ƙalilan a cikin wannan makon, ga shi yanzu kuma ta cigaba da aika aikar taimakon masu wawushe kayan, wanda zai ci gaba da yunwatar da Palasɗinawa sama da miliyan 2.

Wannan hari na Isra'ila kan ayarin motocin kayan agajin ya auku ne ranar Alhamis a daidai lokacin da ayarin motocin ke kan hanyar zuwa wajen ajiyar kayan, Isra'ila ke ta hari motocin a yayin da suke wuce wa ta sha-tale talen Salahaddin Street kusa da Deir al-Balah a tsakiyar zirin Gaza.

Ma su wawason kayan agajin ne suka fara buɗe ma ayarin motocin wuta da bindigu domin ƙwace kayan agajin.

A yayin da masu baiwa motocin kariya suka yi kokarin daƙile harin shine sojin Isra'ila suka fara na su hare haren ta hanyar amfani da jiragen sama akan waɗannan masu bada kariya su 6.

Da faruwar lamarin fararen hula da motocin agaji suka garzaya domin kai É—auki suma aka buÉ—e masu wuta.

Duk da cewa Isra'ila ta bar kusan motoci 200 sun shiga Gaza a wannan makon, amma wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na Reuters suka wallafa ya nuna cewa har zuwa ranar Alhamis kayan tallafin basu fara isa wuraren dafa abinci, idajen gasa gurasa, asibitoci harma da kasuwanni, kamar yadda masu kula da wadannan wuraren suka tabbatar ma Reuters.

A cewar daraktan hukumar "World Food Programme" (WFP) ya bayyana cewa "Babu É—aya daga cikin kayan tallafin nan da ya isa hannun mutanen Gaza.

Post a Comment

Previous Post Next Post