Kamfanonin Jiragen ƙasashe da na ƴan kasuwa sun dakatar da jigilar fasinjoji zuwa haramtacciyar ƙasa
Daga - Mahadi Tukur Almizan
Sakamakon ci gaba da kai hare hare da rundunar Ansarullah ta Yemen ke yi a tashar jiragen saman Isra'ila kamfanonin jiragen sun dakatar da jigilar fasinjoji har sai abinda hali yayi.
Ko a yau juma'a rundunar ta Ansarullah ta kai hari tashar jiragen ta Ben Gurion dake Tel Aviv kamar yadda rundunar ta fitar da sanarwa a yau, in da suka bayyana cewa sun harba Hypersonic ballistic missile, wannan harin shine na uku da suka kai ma tashar jiragen cikin awanni 24.
Rundunar ta Ansarullah ta bayyana cewa wannan hari da suka kai ya cimma nasara domin kuwa ya saka ma ƴan mamaya razani da firgici sun yi ta guje gujen ɓoyewa a maɓuya.
Da sanyin safiyar yau juma'a ne dai aka ji ƙaraurawar ankararwa na tashi a birnin Tel Aviv sakamakon harin missile ɗin na Yemenawa duk da cewa rundunar sojin haramtacciyar ƙasa sun yi iƙirarin cewa sun yi nasarar kakkaɓo missile ɗin.
A lokacin da harin ya auku miliyoyin ƴan mamaya ne suka riƙa ruguguwar shiga wurin ɓoyo a cewar kafar yaɗa labarai ta Hebrew Media.
Rundunar ta Ansarullah dai ta ƙara ta'azzara hare haren ta a wannan tashar jirage ta Ben Gurion tun lokacin da tayi nasarar harba wani ballistic missile da yayi babbar ɓarna a tashar, tun a farko farkon wannan wata na Mayu, kuma rundunar ta gargaɗi jiragen ƙasashen waje cewa wannan tashar fa babu sauran tsaro.
Sakamakon haka kamfanonin jiragen sama na ƙasa da ƙasa masu yawa ne suka dakatar da jigilar mutane zuwa Isra'ila, ciki har da kamfanin Lufthansa Group da kuma kamfanin ITA na ƙasar Italiya sun dakatar da jigilar fasinjoji har zuwa ranar 8 ga watan Mayu.
Shi ma kamfanin jiragen sama na Seychelles ya dakatar da jigilar fasinjoji a watan June da July, ya tabbatar ba zai dawo aiki ba har sai August
A ranar Litinin ɗin da ta gabata shima CEO na kamfanin Ryanair mai suna Michael O'Leary ya bayyana ma manema labarai cewa "Hakurin kamfanin wajen zuwa Isra'ila da ɗauko fasinja daga Isra'ilar ya ƙare saboda rashin tsaro" ya kara da cewa idan har aka cigaba a haka to lallai kamfanin zai canza akalar harkar jigilar ta shi daga Isra'ila.
Hakanan kamfanonin kasashe da yawa sun dakatar da jiragen su zuwa haramtacciyar ƙasa ciki har da Air India, Air Canada da kuma United Airlines.
A yau juma'a rediyon sojin Isra'ila ya bayyana cewa kamfanin jiragen sama na Birtaniya "British Airline" ya dakatar da jigilar fasinjoji har zuwa ƙarshen watan July.
