Offline

Hare Haren Isra'ila A Makarantu: Aƙalla Palasɗinawa 103 Isra'ila Ta Kashe A Makarantun Da Palasɗinawa Ke Zaman Gudun Hijira

 


Ciki harda ahali guda baki ɗaya.


Isra'ila ta ƙara tsananta ta'addancin ta a zirin Gaza tun bayan da ta fitar da sanarwar mamaye zirin Gaza baƙi ɗaya a ranar Litinin.


Jiragen yaƙin Isra'ila sun hari makarantu biyu mabanbanta da Palasɗinawa ke zaman neman mafaka, harin ya yi sanadiyar rayukan Palasɗinawa 49, mafi yawan su mata ne da ƙananan yara, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta WAFA news agency a ranar Litinin.


Ma'aikatar lafiya ta Palasɗinawa ta fitar da rahoton cewa jiragen na Isra'ila sun hari makarantar Abu Hamisa dake sansanin gudun hijira na Al-Bureij dake tsakiyar Gaza a daren shekaranjiya wanda yayi sanadiyar rayukan Palasɗinawa 33 tare da raunata wasu 73.


Hakanan a safiyar jiya wasu jiragen Isra'ila biyu sun hari makarantar Al-Karama dake unguwar Al-Tuffah a gabashin birnin Gaza inda suka kashe Palasɗinawa 16 tare da raunata wasu gomomi.


Daga cikin waɗanda aka kashe akwai ɗan jarida Nour Abdu, ofishin yaɗa labarai na Gaza ya bayyana cewa da wannan adadin Palasɗinawan da aka kashe ya cika 213.


👉

Hakanan wani hari da suka kai wata makaranta a Arewacin Gaza yayi sanadiyar rayukan Palasɗinawa 13 a jiya Laraba.


Aƙalla Palasɗinawa 22 ciki harda ƙananan yara 7 suka yi shahada a ranar Talata sakamakon harin da jiragen Isra'ila suka sake kaiwa makarantar dake sansanin gudun hijira na Al-Bureij.


👉

Post a Comment

Previous Post Next Post