Daga - Mahadi Tukur Almizan
Aƙalla fursunoni 70 ƴan Afirka dake tsare a wani gidan yarin kasar Yemen ne suka rasa rayukansu tare da aƙalla mutum 50 da suka tsira da raunuka, sakamakon wani mummunan hari da Jiragen yaƙin Amurka suka kai a wani gidan yari dake yankin Saada kamar yadda kafafen yaɗa labarai suka labarto.
Kafar yaɗa labarai ta Almasirah ta wallafa a jiya Litinin cewa Amurka ta kai harin ne a wani wurin tsare ƴan gudun hijira da suka fito daga ƙasashen Afirka, wanda ke ɗauke da aƙalla fursunoni 115.
Jami'an hukumar agaji ta Civil defense sunyi aiki ba ƙaƙƙautawa domin kashe wutar da ta turnuƙe sakamakon harin tare da ceto rayukan waɗanda ke cikin gidan yarin tare da kai su cibiyoyin kula da lafiya.
Wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta ya nuna yadda wurin ya turnuƙe ana iya ganin jikkunan mutane da suka tarwatse.
Kuna iya kallon bidiyon anan 👉https://rb.gy/fr9gp9
Hukumomin cikin gida sun bayyana cewa akwai wani daga cikin missiles É—in da jiragen na Amurka suka harba ya faÉ—o ba tare da ya tarwatse ba a kusa da gidan yarin.
Ministan harkokin cikin gida na ƙasar ta Yemen yayi Allah wadai da wannan hari inda ya bayyana shi a matsayin "Cikakken laifin yaƙi" da kuma saɓa ma dokokin ƙasa da ƙasa.
Ministan ya bayyana cewa wannan gidan yari da Amurka ta kaima hari yana ƙarƙashin kulawar hukumar ƴan gudun hijira ta ƙasa da ƙasa 'International Organization For Migration ' da kuma hukumar agaji ta duniya 'International Federation Of Red Cross And Red Crescent Societies '
Wannan ya nuna cewa Amurka ta kai wannan hari ne tana sane cewa keta dokokin ƙasa da ƙasa ne.
Kafar yaɗa labarai ta Almasirah ta bayyana cewa an tabbatar da rasa rayukan fursunoni 68 kuma ana tsammanin adadin zai iya wuce haka domin ana cigaba da zaƙulo jikkunan mutane a muhallin.
Hedkwatar tsaron Amurka ta Afirka da ake kira US Central Con (US CENTCON) bata bada cikakken bayani ba akan wannan hari sai dai ta ce: "Domin kiyaye bayanan tsaro mun taƙaita bada bayanai akan ayyukan da muke gudanarwa a yanzu ko wadanda zamu gabatar anan gaba".

