A safiyar yau, sojojin mamaya na Isra’ila sun harbe wani matashi ɗan Falasdinu a sansanin ’yan gudun hijira na Jalazone da ke Ramallah, wanda ya kai ga shahadarsa, yayin kai hare-hare a wasu sassan Yammacin Kogin Jordan (West Bank) a lokaci guda.
Matashin mai suna Malek Ali al-Hattab, mai shekaru 19, ya yi shahada ne bayan ya samu harbin harsashi daga sojojin Isra’ila a unguwar al-Batn da ke cikin sansanin Jalazone, arewacin Ramallah, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu ta tabbatar.
Malek ya jikkata tare da wasu matasa guda biyu a lokacin harin da aka kai da sassafe.
A lokaci guda, sojojin mamaya sun kutsa garin Nablus a ƙasar Yamma, inda suka kewaye wani gida da ke kan titin Tal Gharb, suka harbe wani matashi sannan suka kama shi.
A garin Ariha (Jericho) kuwa, sojojin sun kutsa ciki suka kuma ci gaba da rufe ƙofofin shiga da fita na garin, suna hana zirga-zirga.
Tun bayan da Isra’ila ta sake ƙaddamar da sabuwar gagarumar hari kan Zirin Gaza a ranar 18 ga Maris, 2025, ta ƙara tsananta hare-harenta kan Yammacin Kogin Jordan.
Mamayar Jenin da Kama Yara
A wani bangare, a ranar Litinin, sojojin mamaya na Isra’ila sun kutsa Asibitin Gwamnati na Jenin (Khalil Suleiman Governmental Hospital) da ke arewacin Yammacin Kogin Jordan, inda suka kama wani yaro.
Shaidu sun shaida wa Kamfanin Labaran Anadolu cewa sojojin Isra’ila sun shiga asibitin har zuwa sashen rajista da gaggawa, inda suka kama yaron.
Bayan haka, sojojin sun tsare wasu ma’aikatan asibitin kafin daga bisani suka janye.
Quds News Network ta kuma ruwaito cewa yaron da aka kama a wajen asibitin shi ne Ahmad al-Awartani.
Wani faifan bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna yadda sojojin Isra’ila suka kutsa wani shagon kasuwanci a wajen asibitin, inda suka fito da wasu samari da karfi, yayin da tashin hankali ke ƙara kamari a yankin.