Daga - Mahadi Tukur Almizan
Domin Ƙwace tashar jiragen ruwa ta Hodeidah daga hannun ƴan Houthi.
Dakarun STC dake samun goyon bayan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) sun shirya karɓe tashar jiragen ruwa dake birnin Hodeidah a daidai lokacin da jiragen Amurka ke cigaba da luguden wuta akan fararen hula a yankunan dake ƙarƙashin ƴan Houthi a ƙasar ta Yemen.
Kafar yaɗa labarai ta "Wall Street Journal" ce ta wallafa labarin shirin na Amurka da Dubai ta hanyar amfani da dakarun na STC a jiya Talata 15 ga watan Afrilu.
A cewar kafar yaɗa labaran ta WSJ wani kamfanin tsaro mai zaman kanshi na Amurka yana aiki tare da dakarun STC na Yemen domin shirya yadda zasu ƙaddamar da hari ta ƙasa, wasu daga cikin waɗanda ake wannan shiri dasu sun bayyana cewa, UAE dake goyon dakarun na STC ne tare da jami'an Amurka sun fara ɗago wannan batu ne harin ƙasa tun makonni da suka gabata.
Anason a kai wannan hari ne a daidai lokacin da jiragen Amurka ke cigaba da harar dakarun Ansarullah na Yemen.
Wani jami'in Amurka ya bayyana ma jaridar ta Wall Street Journal cewa Amurka ta kai hare hare sama da 350 a jerin hare haren da take kaiwa dakarun na Ansarullah, kuma wai a cewar shi sun raunana rundunar ta Ansarullah sakamakon waɗannan hare hare.
Yadda aka tsara wannan hari da za a kai ta ƙasa , ƴan barandan na UAE da ake kira STC wato "Southern Transitional Council" zasu jibge dakarun su a arewa da kudancin gaɓar ruwan Yemen daga nan sai suyi ƙoƙarin ƙwace tashar jiragen ruwa ta Red Sea dake birnin na Hodeidah, kamar yadda wata majiya mai alaƙa da dakarun masu goyon bayan dubai ya wallafa.
👉
Two indications of the imminent US-led ground confrontations in Yemen.
— Ahmed Hassan 🇾🇪 أحمد حسن زيد (@Ahmed_hassan_za) April 14, 2025
1. Today's US bombing focused on the eastern regions under Sana'a's control. Specifically, the bombing targeted defensive lines in Ma'rib and Al-Jawf governorates.
This indicates that US aircraft have begun… pic.twitter.com/nj5lehRWEg
Idan wannan yunƙuri yayi nasara to zai tilasta ma dakarun Ansarallah janye wa daga bakin gaɓar da suke harbin jiragen dako masu alaƙa da Isra'ila.
Sai da wata rundunar da Saudi Arabia ke goya ma baya a ƙasar ta Yemen da ake kira (Presidential Leadership Council " PLC sun bayyana cewa bazasu shiga cikin wannan aikin na ƙoƙarin ƙwace tashar ta Hodeidah daga hannun ƴan Houthi ba, jami'an Saudi Arabia dake goyon bayan wannan runduna ne suka faɗi haka a sirrance.
Gwamnatin da rundunar Ansarullah ta kafa (Ansarallah Led National Salvation Government) na rike da mafi yawan faɗin ƙasar ta Yemen wanda ya haɗa harda babban birnin ƙasar wato Sana'a da kuma birnin Hodeidah mai babbar tashar jiragen ruwa, yayinda sauran wasu bangarorin ƙasar kuma ke hannun ƴan barandan da UAE da Saudi Arabia ke goya ma baya tun bayan kawo karshen yaƙin basasar Yemen a shekarar 2022.
Wannan yunkuri zai iya dawo da yaƙin basasa a ƙasar ta Yemen wanda aka fara tun shekarar 2014 aka kawo karshen shi a 2022 sakamakon yarjejeniyar zaman lafiya da majalisar ɗinkin duniya ta jagoranta.
Ba wannan bane karon farko da aka yi ƙoƙarin ƙwace tashar jiragen ta Hodeidah ba, domin kuwa a shekarar 2018 masarautar Saudi Arabia ta ƙaddamar da hare hare har uku akan dakarun Ansarallah domin ƙwace wannan tashar jiragen ta Hodeidah.
A lokacin yaƙin basasar rundunonin dake samun goyon bayan Saudi Arabia da UAE sun kashe kusan mutum dubu 15 (15,000) sakamakon Boma bomai da suke jefawa, a lokaci guda kuma sojin ruwan Saudi Arabia suka toshe tashoshin jiragen ruwa na Yemen wanda ya hana shigar kayan tallafi da jin ƙai, wanda hakan ya sake sanadiyyar rasa rayukan wasu dubunnan mutane a ƙasar.
Tun a watan Nuwamba na shekarar 2023 ne dai rundunar Ansarallah ta shelanta fara harar jiragen dako na Isra'ila da masu alaƙa da ita domin tilasta Isra'ila dakatar da kisan kiyashi kan Palasɗinawa a Gaza.
