Offline

Kisan Ƙare Dangi A Deir Al-Balah : Yadda Isra'ila Ta Kashe Mutum 6 Ƴaƴan Mutum Ɗaya A Lokaci Guda

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan


Aƙalla Palasɗinawa 9 ne suka yi shahada a wani ƙazamin hari da jiragen Isra'ila suka kai Deir Al-Balah dake tsakiyar Gaza a ranar Lahadin da ta gabata.


Daga cikin waɗannan shahidai 9 akwai Maza shida ƴaƴan Abu Mahadi, kamar zaku gani a bidiyon dake ƙasa mahaifin su ne ke yi masu sallar janaza.

👉

Kafafen yaɗa labarai na cikin gida sun bayyana cewa jiragen Isra'ila sun jefa missiles ne akan wata motar fararen hula wanda ya shahadantar da waɗannan mutane.


Wani Bafalasɗine ɗan rajin kare haƙƙin ɗan Adam mai suna Ramy Abdu ya bayyana cewa "Wannan mota na ɗauke dasu zuwa ga rayuwa, amma Isra'ila ta zaɓi ta kaisu ga mutuwa" ya bayyana haka ne a shafin shi na X (Twitter).


Wannan hari da ya shahadantar da iyalan Abu Mahadi ya biyo bayan hare haren da Isra'ila ta kai yammacin Deir Al-Balah da Khan Yunis.


Hakanab kafin asubahin ranar Isra'ila ta hari sansanin gudun hijira na Al-Mawasi, inda ta tarwatsa tantunan Palasɗinawa dake zaune a sansanin har an samu Shahidai.


Hakanan jami'an lafiya sun bayyana cewa Isra'ila ta hari wata mata ta hanyar amfani da Drone a Jabalia dake arewacin zirin Gaza.


A wancan hari da suka kai yammacin Khan Yunis sun hari gidan Daraktan ƴan sanda na Gaza mai suna Mohammad al-Darbashi.


A cewar sojin Isra'ila duk waɗannan hare haren domin tursasa Hamas ne ta saki kamammun da take tsare dasu.

Post a Comment

Previous Post Next Post