Akwai manyan jami'an Isra'ila da suka sha alwashin ko ƙwayar alkama bazata shiga zirin Gaza ba, a daidai lokacin da matsananciyar yunwa ta mamaye faɗin zirin na Gaza.
Isra'ila ta hana shigar motocin kayan abinci shiga Gaza kwanaki 37 kenan a jere wanda ya fara daga ranar 07 ga watan March zuwa jiya 07 April.
Wata takarda da shugabannin hukumomin agaji guda bakwai na majalisar É—inkin duniya suka fitar ciki harda OCHA da kuma World Food Programme sun bayyana cewa "Samada da mutane miliyan biyu da dubu É—ari (21.Million) ne Isra'ila ta tarfa a zirin na Gaza suna masu fuskantar matsananciyar yunwa gami da hare haren boma bomai, babu abinci babu magani, babu sutura babu man fetur".
Sun kara da cewa "Muna kallon laifukan yaƙi ƙiri ƙiri a Gaza wanda suka keta alfarmar ɗan Adam, muna kira ga shugabannin duniya su gaggauta ɗaukar mataki domin ganin Isra'ila ta ɗabbaƙa dokokin ƙasa da ƙasa"
Isra'ila dai ta datse shigar kayan tallafi shiga Gaza ne tun a watan March domin tursasa Hamas karɓar sabuwar yarjejeniyar da Amurka ta rubuta domin shiga fuska ta biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas a watan January.
Ana cikin haka kwatsam a ranar 18 ga watan na March Isra'ila ta dawo kai hare hare kan Palasɗinawa inda ta kashe aƙalla mutum 1,400 aƙallam 400 daga ciki ƙananan ne, wannan ya gudana ne cikin makonni 3 da suka gabata zuwa yau wato daga 18 March.
👉
All bakeries in Gaza have now shut down and the World Food Programme has announced it has just 14 days of food left in the Strip before operations stop entirely. Since March 2, 2025, Israel has blocked all aid and closed every crossing into Gaza. For 30 consecutive days, no food,… pic.twitter.com/dVCR0EMrYj
— Translating Falasteen (Palestine) (@translatingpal) April 1, 2025
Haryanzu dai Isra'ila na nan akan bakarta na hana kayan tallafi shiga zirin Gaza kamar yadda Bezalel Smotrich ministan kuÉ—i na haramtacciyar kasa ya jaddada a ranar Litinin cewa lallai ba zasu bari komai ya shiga Gaza ba, yayi wannan batun ne bayan wasu kafafen yaÉ—a labarai na Isra'ila sun labarto cewa rundunar sojin Isra'ila na shirin sassauta hana shigar kayan tallafin.
Shi Smotrich ɗin ne ya bayyana cewa "Ko ƙwayar Alkama bazata shiga zirin Gaza ba".
Sakamakon hana shigar kayan abinci Gaza aƙalla gidajen hasa biredi 27 aka rufe wanda hukumar World Food Programme ke tallafawa, an rufe su ne sakamakon rashin fulawa da Gas ɗin girki.
A ranar Lahadin da ta gabata mai magana da yawun hukumar UNICEF Kazem Abu Khalaf ya sanar cewa an rufe Wuraren bayar da tallafin abincin yara aƙalla guda 21 a Gaza saboda hare haren Isra'ila.
Isra'ila dai ta kashe sama da Palasɗinawa dubu hamsin daga 07 October 2023, wasu dubunnai kuma na ƙarƙashin baraguzan gine gine.
Freedom Fighters Ng
