ÆŠan jarida Ahmad Mansour ya yi shahada bayan ya samu mummunan rauni da Æ™una sakamakon harin jiragen yakin Isra’ila da suka kai kan wani tantin ’yan jarida da ke kusa da Asibitin Nasser Medical Complex a Khan Younis, Kudancin Gaza.
Rahotanni sun bayyana cewa ya rasu da daren jiya a asibiti.
Tun da safiyar ranar Litinin, wani É—an jarida É—an Falasdinu da wani saurayi sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon harin da jiragen Isra’ila suka kai kan tantin ’yan jarida a wajen asibitin Nasser.
Wakilin Al Mayadeen ya tabbatar da cewa É—an jarida Hilmi al-Faqawi, wakilin Palestine Today, da saurayi mai suna Yousef al-Khazindar sun yi shahada. Daga cikin ’yan jaridar da suka jikkata akwai Ahmad Mansour, Hassan Islayh, Ahmad al-Agha, Mohammed Fayek, Abdullah al-Attar, Ihab al-Bardini, Mahmoud Awad, da Majed Qudaih.
Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Falasdinu ta fito fili ta la’anci wannan hari, tana bayyana cewa harin da Isra’ila ta kai kan tantin ’yan jarida a Khan Younis ya sabawa duk wata doka ta Æ™asa da Æ™asa, tana kuma alhinin mutuwar É—an jarida Hilmi al-Faqawi.
Kisan Ahmad Mansour ya haifar da kakkausar suka daga Æ™asashen Larabawa da na duniya baki É—aya. Hukumar Duniya mai Kare Haƙƙin Al’ummar Falasdinu ta bayyana wannan harin a matsayin laifi na yaÆ™i, wanda aka shirya domin dakile yancin kafafen watsa labarai da kuma hana bayyanar gaskiyar abin da ke faruwa a Gaza.
Masu amfani da kafafen sada zumunta sun bayyana É“acin ransu, suna mai jaddada cewa harin Isra’ila kan ’yan jarida ya kasance wata manufa ta ci gaba da take haƙƙin É—an adam, duk da cewa dokokin kare lafiya da zaman lafiya na duniya na kare lafiyar ’yan jarida a lokutan rikici.
A ranar 24 ga Maris, rundunar mamayar Isra’ila ta kai hare-hare kan ’yan jarida biyu – Mohammed Mansour da Hussam Shabat – a lokuta daban-daban, yayin da suke gudanar da aikinsu a cikin Gaza.
Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya tabbatar da cewa tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023, ’yan jarida da aka kashe sun haura 210.
Duk da Æ™arar muryoyin Æ™asashen duniya da Æ™ungiyoyin kare haƙƙin É—an adam, har yanzu Isra’ila na ci gaba da kai hare-haren ta a Gaza. Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa daga 18 ga Maris zuwa 7 ga Afrilu, 2025, Isra’ila ta kashe Falasdinawa 1,391 tare da jikkata 3,434. Tun daga 7 ga Oktoba 2023 zuwa yanzu, adadin shahidan ya kai 50,752, yayin da masu jikkata suka haura 115,475.