Offline

Iran Ta Yi Gargaɗi: “Mun Shirya Tsaf Domin Yin Yaki”

Shugaban Rundunar Kare Juyin Juya Hali ta Iran (IRGC), Manjo Janar Hossein Salami, ya bayyana a ranar Asabar cewa ƙasarsu ta shirya tsaf domin yin yaƙi idan har aka tilasta mata yin hakan.

“Ba ma jin wani fargaba game da yaƙi kwata-kwata. Ba za mu fara yaƙi ba, amma muna da cikakken shiri domin tunkarar kowanne irin yaƙi,” in ji shi, kamar yadda kafar labarai ta gwamnati, IRNA, ta ruwaito.

Ya kara da cewa, “Mun koyi dabarun cin galaba a kan makiya, kuma ba za mu ja da baya ba.”

Janar Salami ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da manyan kwamandoji da shugabannin IRGC a hedkwatarsu, inda ya yi nazari kan shekarar Fars ta da ta gabata (wanda ta ƙare a ranar 20 ga Maris, 2025), yana cewa shekarar ta kasance cike da rikice-rikice masu tsanani.

“A wannan shekara, dukan dakarun kafirai sun hada kai suna yakar rundunar Musulunci, suna amfani da dukkan karfinsu a fagen fama,” in ji shi.

Ya kuma yi nuni da kisan wasu manyan kwamandojin IRGC da suka hada da Birgediya Janar Mohammad Reza Zahedi da Birgediya Janar Haj Rahimi, da suka rasa rayukansu a harin da Isra’ila ta kai a ofishin jakadancin Iran da ke Damascus bara.

“Bayan harin da Yahudawa suka kai ofishinmu a Damascus, mun yanke wasu muhimman tsare-tsare domin fuskantar abokan gaba kai tsaye — wata muhawara da za ta iya haifar da tasiri a duniya baki ɗaya. A karon farko cikin tarihin Musulunci, babban rikici irin wannan ya fara samuwa,” in ji shi.

Wannan bayani ya fito ne a daidai lokacin da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ke ci gaba da barazanar cewa za a kai hari kan Iran idan har ba ta yarda da tattaunawa kai tsaye kan shirinta na nukiliya ba, a karkashin manufar “Matsin lamba mafi girma.”

Post a Comment

Previous Post Next Post