Daga - Mahadi Tukur Almizan
Da safiyar jiya 13 ga watan Afrilu ne Isra'ila ta harba missiles guda biyu kan asibitin Al-Ahli Baptist Hospital dake zirin Gaza, hakan yasa asibitin ya tashi daga aiki.
👉
Early on Sunday, Israel bombed Al-Ahli Baptist Hospital in Gaza City with two missiles, rendering it out of service and destroying the intensive care and surgery departments.
— The Cradle (@TheCradleMedia) April 13, 2025
The Baptist Hospital is the last functioning hospital in Gaza City. pic.twitter.com/bfcG2U0LK5
Wannan asibiti na Al-Ahli shine muhallin kula da lafiya na ƙarshe da ya rage yana aiki a birnin Gaza, zaku iya ganin yadda harin na Isra'ila ya tarwatsa asibitin a bidiyon dake ƙasa.
👉
This is what US weapons and ammunition did to Al-Ahli Baptist Hospital in Gaza City last night.#GazaHolocaust pic.twitter.com/6FTkG3DHhJ
— Seyed Mohammad Marandi (@s_m_marandi) April 13, 2025
Ɓangarorin asibitin da suka tarwatse sun haɗa da bangaren Emergency,trauma, laboratory, pharmacy da kuma sashen radiology a cewar daraktan asibitin.
Ya ƙara da cewa "A halin yanzu wannan asibiti ta daina aiki sakamakon hare haren Isra'ila" ya kuma ƙara da cewa akwai bukatar a matsa ma Isra'ila ta bari a shigo da kayan agaji su shigo Gaza domin cigaba da aikin lafiya tare da baiwa asibitin cikakkiyar kariya.
Akwai wani yaro daga cikin waɗanda aka kwantar a asibitin wanda ya tsira da rauni amma a yayin ɗauke shi daga asibitin shima ya rasa ranshi.
Sojin Isra'ila sun yi iƙirarin cewa wai sun hari muhallin dakarun Hamas ne dake ƙarƙashin asibitin, kamar yadda hukumar hukumar sojin ta Isra'ila haɗin gwuiwa da Shin Bet suka bayyana cewa su suka kai harin bisa wannan dalilin.
Sai dai hukumar Civil defense ta Gaza ta bayyana cewa wannan iƙirarin na cewa akwai muhallin dakarun Hamas a asibitin zancen ƙarya ne.
Ba wannan bane karon farko da Isra'ila ta hari wannan asibiti na Al-Ahli Baptist Hospital, ta hare shi a lokuta mabanbanta tun bayan barkewar yaƙin.
A jiya Lahadi ma'aikatar lafiya ta Gaza ta bayyana cewa an samu shahidai 11, da masu raunuka 111.
A ranar 17 ga watan Oktoban shekarar 2023 an samu daruruwan shahidai fararen hula sakamakon harin da Isra'ila ta kai wannan asibiti, duk da Isra'ilar ta musanta alhakin kai harin, inda ta ce wai ƴan muƙawama ne suka yi harba ma asibitin rocket.
Hakanan sauran asibitocin Gaza kamar Indonesian Hospital, Kamal Adwan da sauran su dake zirin Gaza duk sun fuskanci hare haren Isra'ila a lokuta mabanbanta.
