- Mahadi Tukur Almizan
Wata sanarwa da dakarun Yemen suka fitar ta bayyana cewa "A matsayin martani ga hare haren da Amurka ke cigaba da kawo wa cikin kasar mu tare da kashe rayukan al'ummar mu, munyi nasarar kakkaɓo jirgi maras matuki (Drone) na Amurka ƙirar MQ-9 a daidai lokacin da yake shawagi a sararin samaniyar gundumar Al-Jawf a hanyar shi ta kai hari".
Sanarwar ta ƙara da cewa "Wannan shine karo na uku da muka yi nasarar kakkaɓo irin wannan jirgi a tsakanin kwanaki 10, kuma na 18 dag fara wannan yaƙi na goyon bayan Palasɗinawa".
Wannan jirgi mara matuƙi na Amurka ƙirar MQ-9 yakai ƙimar dala miliyan 30 ( $30 Million) kowanne ɗaya, hakan na nufin a tsakanin kwanaki 10 dakarun na Ansarullah sun yi ma Amurka asarar dala miliyan 90.
Dakarun na Yemen sun ƙara jaddada aniyar su ta cigaba da goyon bayan Palasɗinawa tare da baiwa ƙasar su kariya gamida da tunkurar duk wani hari akan al'ummar su.
Sun bayyana cewa a shirye suke tsaf domin tunkarar duk wani yunkuri na keta alfarmar kasar su da hana su zaman lafiya, kuma bazasu daina kai hare haren goyon bayan Palasɗinawa ba har sai Isra'ila ta dakatar da hare haren ta akan al'ummar Gaza, a cewar su.
©️ Freedom Fighters Ng
