Offline

Isra'ila Ta Kashe Mutum 71 A Lebanon Daga Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Zuwa Yau

 



Daga - Mahadi Tukur Almizan


Hukumar kare haƙƙin ɗan Adam ta majalisar dinkin duniya ta fitar da wata sanarwa a shekaranjiya Talata wadda ke cewa Isra'ila ta kashe fararen hula ƴan ƙasar Lebanon har mutum 71 tun daga yarjejeniyar tsagaita wuta da aka ƙulla a ranar 27 ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata.


Hukumar ta bayyana cewa 14 daga cikin shahidan Mata ne, yayinda 9 daga ciki kuma ƙananan Yara ne, hare haren na Isra'ila kuma sun hana sama da mutum dubu 92 dawowa gidajen su.


Mai magana da yawun wannan hukumar kare hakkin dan Adam ta majalisar É—inkin duniya Thameen al-khaeetan ya bayyana wa manema a can birnin Geneva cewa Isra'ila ta hari kudancin birnin Beirut har sau biyu a lokuta mabanbanta, kuma duka wuraren da ta hara suna kusa da makarantu.


Ka a ranar 1 ga wannan wata da muke ciki na Afrilu Isra'ila ta hari gine ginen unguwar fararen hula a kudancin na Beirut wanda yayi sanadiyar shahadar mutum 2 tare da raunata wasu gami da rusa muhallai.


Hakanan wasu kwanaki biyu a ranar 3 ga wata Isra'ila ta sake kai hari ginin sabuwar cibiyar lafiya da aka gina badaɗewa wadda ke ƙarƙashin Islamic Medical Association anan kudancin birnin na Beirut a harin Naqoura, wannan hari ya tarwatsa motocin agaji wato Ambulance har guda biyu.


A kudancin Lebanon É—in Isra'ila ta kaddamar da hare hare a ranakun 4 da 8 ga watan nan na Afrilu inda aka samu Shahidai 6 da kuma masu raunuka da dama.


Thameen al-khaeetan ya bayyana cewa hare haren Isra'ila na cigaba da sauka kan gine ginen fararen hula tun bayan da aka ƙulla yarjejeniyar ta tsagaita wuta, inda take harar gidaje,muhallan kula da lafiya, hanyoyi kai harma da Cafe a garin Aita al-Shaab.


Ko a jiya Talata sai da Isra'ila ta kai hari garin Aitaroun dake gundumar Bint Jbeil a kudancin Lebanon, wanda yayi sanadiyar shahadar mutum 3 ciki harda ƙaramin Yaro.

Post a Comment

Previous Post Next Post