Daga - Mahadi Tukur Almizan
Wata majiya daga sashen lafiya na Gaza ta labarta ma kafar yaɗa labarai ta Aljazeera cewa a cigaba da hare haren Isra'ila a zirin Gaza shahidai 34 aka samu a jiya juma'a.
Wani hari da Isra'ila ta kai shagon aski a tsakiyar Khan Yunis dake kudancin Gaza ya yi sanadiyar shahadar Palasɗinawa aƙalla 6, ciki har da ƙananan yara 2.
Hakanan wani hari da Isra'ilar ta kai a Khan Yunis ɗin ya kashe ƙananan yara a daidai lokacin da suke ɗiban ruwa.
Hare haren na Isra'ila sun ƙazanta domin kuwa an riƙa kai mata da ƙananan yara asibiti ko gane su ba a iya yi kamar yadda Aljazeera ta wallafa.
Isra'ila dai na cigaba da ƙara ƙaimi wajen zubar da jinin raunana a kowace rana.
Ko a yammacin shekaranjiya Alhamis an samu wasu shahidai 10, ciki harda iyalan matashin ɗan jaridar nan mai suna Tamer Miqdad, inda aka kashe shi tare da ƴar shi da wasu ahalin shi sakamakon wasu hare hare da Isra'ila ta kai unguwar Tal al-Zaatar dake Jabalia a arewacin Gaza.
Hakanan a ranar Talata a wani hari da Isra'ila ta kai a tantunan masu gudun hijira dake Khan Yunis yayi sanadiyar shahadar Palasɗinawa 15.
Adadin ƴan jaridu da Isra'ila ta kashe daga fara wannan kisan kiyashi yakai 213.
Daga dawowar Isra'ila cigaba da kai hare hare kan Palasɗinawa a watan da ya gabata sun kashe sama da Palasɗinawa 1,691
👉
Israel committed a massacre in south Gaza's Khan Yunis, targeting the tents of displaced Palestinians, which went up in flames, killing at least 15 people. pic.twitter.com/zZuDSEyVaq
— The Cradle (@TheCradleMedia) April 17, 2025
A gefe guda kuma sun rufe duk wata mashiga zuwa zirin Gaza da ake shigar da kayan jin ƙai da tallafi, wannan yasa asibitocin dake Gaza sun rasa kayan aikin ceton rayukan Palasɗinawa.
Ko a ranar Laraba ministan tsaron Isra'ila mai suna Israel Katz ya jaddada cewa ba zasu bari a shiga da kayan agaji zirin Gaza ba kwata kwata, domin wannan wata hanya ce da suke aiki da ita wajen tursasa Hamas.
A lokaci guda kuma Isra'ila na cigaba da mamaye zirin na Gaza, domin kuwa zuwa yanzu Isra'ila ta mamaye aƙalla kaso hamsin (50%) na Gaza.
Ministan tsaron Isra'ila Israel Katz ya jaddada cewa sojin haramtacciyar ƙasa zasu cigaba da mamaye zirin na Gaza, yayi wannan kalamai ne bayan da sojoji suka karbe iko da sabuwar Morag wadda ta raba kudancin birnin Rafah da birnin Khan Yunis.
