Bayan wata yarjejeniyar tsagaita wuta mai rauni da ta ɗauki kusan wata biyu, Isra’ila ta sake kaddamar da hare-haren ta da matsanancin ruwan bama-bamai a Gaza, wanda ya yi sanadin shahadar mutum 254 da jikkatar fiye da 440, da dama cikin yanayi mai matuƙar tsanani, in ji Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ranar Talata, yayin da aka ayyana dokar taɓaci.
A baya, Ofishin Yaɗa Labarai na Gwamnatin Gaza ya sanar da cewa fiye da mutum 322 sun mutu ko sun bace cikin sa’o’i biyar kacal, yayin da wasu da dama suka jikkata.
A cewar wakilin Al Mayadeen, Isra’ila ta sake kai sabon gagarumin hari ta sama kan biranen Gaza, inda wani hari mai muni ya fi shafa yankin gabashin Gaza.
Hare-haren Isra’ila sun shafi gidaje, sansanonin ‘yan gudun hijira, da yankunan fararen hula
Jiragen yaki na Isra’ila sun ragargaza gidaje a Rafah, kudancin Gaza, da arewa maso gabashin sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat. A lokaci guda, dakarun artileriya na Isra’ila sun yi luguden wuta a garin Al-Fukhari, gabashin Khan Younis.
Wakilinmu ya tabbatar da cewa titunan Gaza sun kasance kufai, yayin da jama’a suka cika da tsoro sakamakon yawaitar jiragen yakin Isra’ila a sararin samaniya.
Kafofin yada labarai na Falasdinu sun ruwaito cewa Manjo Janar Mahmoud Abu Watfa, Mataimakin Ministan Cikin Gida a Gaza, ya mutu sakamakon wani hari da Isra’ila ta kai a birnin Gaza.
Haka nan, sojojin mamaya na Isra’ila sun bayar da umarnin ficewa daga wasu unguwanni a Gaza, abin da ke kara jefa jama’a cikin halin rudani.
Isra’ila ta keta yarjejeniyar tsagaita wuta
A cewar kungiyar Hamas, tana ci gaba da tattaunawa da masu shiga tsakani dangane da halin da ake ciki, inda ta jaddada cewa tana da niyyar ganin yarjejeniyar tsagaita wuta ta cika gaba daya, kamar yadda kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito.
A gefe guda, Ofishin Yaɗa Labarai na Gaza ya yi kaca-kaca da Isra’ila, yana mai cewa tana ci gaba da take dokokin kasa da kasa da na jinƙai, tare da aikata kisan kiyashi kan fararen hula.
Rahotanni sun nuna cewa Isra’ila ta rufe mashigar Rafah, abin da ya haddasa matsananciyar wahala ga al’ummar Gaza fiye da miliyan 2.4, waɗanda aka hana abinci, magunguna, ruwa, madarar jarirai, da sauran kayayyakin more rayuwa.
Saboda halin tsaro mai tsanani da kuma karancin motocin daukar marasa lafiya, ana fuskantar matsalar jigilar gawarwaki zuwa asibitoci, in ji Ofishin Yaɗa Labarai na Gaza. Mafi yawan wadanda suka rasa rayukansu mata ne, yara da tsofaffi, wanda ofishin ya bayyana a matsayin kisan kiyashi da ke cin mutum, kasa, da tarihi.
Rashin kayayyakin asibiti na kara ta’azzara rikicin
Wannan bala’i yana faruwa ne yayin da tsarin kiwon lafiya na Gaza ke neman durkushewa sakamakon katangar hana shigowar kayayyakin lafiya da agajin jinƙai, abin da ke barazanar dakatar da dukkan ayyukan asibiti.
Dokta Mohammad Abu Salmiya, darektan Asibitin Al-Shifa, ya bayyana cewa Gaza na fuskantar mummunan matsalar rashin magunguna da kayan jinya, inda ya bayyana halin da ake ciki da cewa mummunan bala’i ne mai cike da tashin hankali.
“Ba mu da isassun wuraren ajiyar gawarwaki,” in ji Abu Salmiya, yana mai cewa ana kashe fararen hula da gangan kuma yana sa ran samun karin gawarwaki da jikkata a cikin ‘yan awanni masu zuwa.
Ya kuma yi gargadi cewa "Duniya ta amince da hallaka Gaza”, yana mai cewa titunan Gaza sun lalace, kuma babu motocin ceto da za su kai ga wadanda suka makale karkashin baraguzai.
A halin yanzu, UNICEF ta tabbatar da cewa hare-haren Isra’ila sun shafi sansanonin ‘yan gudun hijira.
Makomar Gaza na kara fuskantar barazana
A matsayin martani ga matsalar tsaro da ke kara dagulewa, Ma’aikatar Ilimi ta Gaza ta sanar da dakatar da dukkan karatu a makarantu da cibiyoyin ilimi har sai baba-ta-gani.
Kafofin yada labarai na Isra’ila sun ruwaito cewa ana ci gaba da tattaunawa kan tsagaita wuta da musayar fursunoni a yayin da ake ci gaba da luguden wuta, yayin da aka hana ministocin Isra’ila su yi karin bayani game da harin da suke kaiwa a Gaza.