Kungiyar Jihadin Musulunci ta Falasdinu (PIJ) ta yi alhinin shahadar Abu Hamza (Naji Abu Seif), kwamandan Brigade al-Quds, wanda aka kashe tare da iyalinsa da na É—an uwansa a wani harin kisan gilla da Isra’ila ta kaddamar.
A cikin wata sanarwa da Æ™ungiyar ta fitar, Abu Hamza an bayyana shi a matsayin “muryar gwagwarmaya, mai tsayin daka wajen kare hakkin al’ummar Falasdinu, kuma gwarzo da ba ya jin tsoro wajen fadin gaskiya.”
Sanarwar ta kuma yi Allah wadai da “wannan kisan gilla da aka aiwatar ta hannun azzaluman ‘yan mamaya, cikin jerin hare-haren ta’addanci da ke cin zarafin al’ummar Falasdinu, ciki har da mata da yara, tare da goyon bayan Amurka.”
"Duk da shiru mai muni daga duniya, wannan zalunci ba zai hana mu ba," in ji kungiyar PIJ, tana mai tabbatar da cewa za ta ci gaba da kare hakkokin al’ummar Falasdinu har sai an kawo karshen wannan zalunci.
Rayuwar Abu Hamza a Gwagwarmaya
Abu Hamza ya zama shahararren mai magana da yawun Brigade al-Quds bayan shekaru na aiki a matsayin mai fafutuka, inda jama’a ke sauraron bayanansa kan matsayar Æ™ungiyar da cigaban al’amura.
A ranar 12 ga Fabrairu, Abu Hamza ya wallafa a shafinsa na Telegram cewa makomar fursunonin Isra’ila da ke hannun gwagwarmaya a Gaza ya dogara ne da matakin da Netanyahu zai É—auka, yana mai zargi da take yarjejeniyar tsagaita wuta.
A watan Yuli 2024, Abu Hamza ya yi wata hira ta musamman da Al Mayadeen, mai taken “Kwana-Kwanan Nan Za a Yanke Hukunci”, inda ya bayyana cewa falasdinawa za su ci gaba da gwagwarmaya har sai an kawo karshen mamaya.
Isra’ila Ta Ci Gaba da Kai Hare-Hare a Gaza
Dakarun Isra’ila sun sake kai gagarumin hari ta sama a Gaza a safiyar Talata, inda suka ragargaza yankunan zama, sansanonin ‘yan gudun hijira, da gine-ginen jama’a, bayan yarjejeniyar tsagaita wuta ta wargaje.
A cewar wakilin Al Mayadeen, adadin shahidan Gaza ya kai mutum 426, yayin da fiye da 600 suka jikkata, da dama cikin halin rai-kwakwai-mutuwar-kwakwai.
Haka nan, kakakin Hukumar Agajin Gaza, Mahmoud Basal, ya bayyana cewa fiye da mutum 400 sun mutu, yayin da kusan 600 suka jikkata, yana mai cewa da dama daga cikinsu na iya rasa rayukansu saboda tsananin raunin da suka samu.