Offline

ISRA'ILA TA SAKE KAI FARMAKI KAN GAZA, TA KARYA YARJEJENIYAR TSAGAITA WUTA



Isra’ila Ta Kaddamar da Mumunan Hari a Gaza Bayan Rushewar Tsagaita Wuta

Dakarun mamaya na Isra’ila sun kaddamar da munanan hare-hare ta sama a fadin Zirin Gaza da safiyar Talata, inda suka kai farmaki kan unguwanni, sansanonin ‘yan gudun hijira, da gine-ginen jama’a, bayan tsagaita wutar da aka kulla ta rushe.

Majiyoyin lafiya na Palasdinawa sun tabbatar da shahadar mutane akalla 205, yawancinsu yara, tare da jikkata daruruwa sakamakon ruwan bama-baman da Isra’ila ke yi.

Wakilin Al Mayadeen da ke Gaza ya ruwaito cewa an kai hare-hare fiye da guda goma a lokaci guda cikin kasa da mintuna goma. Hare-haren sun fi muni a Khan Younis da Rafah, inda rokokin Isra’ila suka ragargaza gidaje, masallatai, makarantu, da wuraren ‘yan gudun hijira.

A yammacin Khan Younis, gobara ta tashi a sansanonin ‘yan gudun hijira bayan bama-baman da aka jefa kai tsaye, inda mutane da dama suka makale a karkashin baraguzan gine-gine.

Hukumar leken asiri ta Shin Bet tare da sojojin Isra’ila sun tabbatar da hare-haren, suna mai cewa an aiwatar da su ne bisa umarnin siyasa. Wani babban jami’in Isra’ila ya bayyana a kafafen yada labarai cewa, “Tsagaita wuta ta Æ™are.”

Kungiyar Hamas ta yi tir da wannan sabon hari, tana zargin Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da ci gaba da yakin kisan kare dangi kan fararen hula marasa makami. Hamas ta bukaci Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa (Arab League), Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi (OIC), da Majalisar Dinkin Duniya (UN) da su dauki matakin gaggawa don dakatar da wuce gona da irin Isra’ila.

Haka kuma, an samu rahotanni na yawaitar motsin sojojin Isra’ila a koridor din Philadelphi da ke kudancin Gaza, abin da ke nuna yiwuwar shiga da sojojin kasa domin kara mamaye yankin.

A gefe guda, Fadar White House ta tabbatar da cewa Isra’ila ta tuntubi Amurka kafin kaddamar da hare-haren, amma ba a bayyana cikakkun bayanai ba.

A halin da ake ciki, kungiyoyin agaji a Gaza na kokawa da matsalar kayan aiki, wanda ke hana su isa wuraren da ake bukatar agaji cikin gaggawa. A sakamakon haka, da dama daga cikin wadanda suka jikkata ba su samun taimakon likita cikin lokaci.

Yanzu haka, duniya na dakon matakin da kasashen duniya za su dauka kan wannan sabon hari da Isra’ila ke ci gaba da aiwatarwa a Gaza.

Majiya: Almayadeen English
Fassara: Freedom Fighters NG

Post a Comment

Previous Post Next Post