Daga - Mahadi Tukur Almizan | Freedom Fighters Ng
Trump ya bayyana cewa shi fa yana nan kan bakar shi na siye da mallake zirin Gaza tare da korar PalasÉ—inawa miliyan 2 dake zaune a Gaza É—in, duk da Allah wadai da PalasÉ—inawa da majalisar É—inkin duniya suka yi.
Ga dai wasu daga cikin kalaman na shi kwabo da kwabo "Ina nan kan bakata na siye da mallake Gaza tare da sake gina ta, zamu iya baiwa wasu ƙasashe a gabas ta tsakiya su gina wani sashe, amma lallai zamu mallake ta, mu tabbatar Hamas bata sake komawa ba" Trump yayi waɗannan kalamai ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a shekaranjiya Lahadi 09 ga wannan wata da muke ciki na February.
Sai dai Trump baiyi bayanin a hannun wanda zasu siya Gaza ba ko kuma tayadda Amurka zata mallaki Gaza ba.
A cewar Mahaukacin kare wai zasu tabbatar sun kyautata rayuwar PalasÉ—inawa da samar masu da zaman lafiya da kwanciyar hankali, a inda ba za a sake kashe su ba, ta yadda ba zasu so komawa Gaza ba, wai a yanzu ma suna komawa ne domin basu da wata mafita bayan wannan.
Bayan wannan batu kuwa Firaministan Haramtacciyar kasa Netanyahu ya jinjina ma Trump bisa wannan yunkuri.
Hukumar kare haƙƙin ɗan Adam ta majalisar ɗinkin duniya ta yi gargadi cewa lallai kwashe Palasɗinawa da karfin tsiya daga zirin Gaza zuwa wani wuri ya saɓa ma dokokin ƙasa da ƙasa.
Hatta al'ummar Amurka a wata kuri'a da aka kaɗa ta nuna cewa aƙalla kaso 47% na mutanen Amurka sunyi yi amanna cewa wannan mummunan kuduri ne, kaso 13% ne kawai ke kallon wannan yunkuri na mallake Gaza a matsayin kyakkyawan kuduri kaso 40 kuwa suna ganin basu natsu da wannan kuduri ba.
Isra'ila dai ta dauki watanni 15 tana jefa boma bomai kan al'ummar Palasɗinu wanda yayi sanadiyar shahadar aƙalla Palasɗinawa 48,000 kafin a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar 19 ga watan January da ya gabata, sai dai wani ƙiyasi ya nuna cewa Isra'ila ta kashe Palasɗinawa akalla 200,000 da taimakon Boma boman da Amurka ke baiwa Isra'ilar.
