Offline

A Jiya Litinin Dakarun Hamas Sun Hallaka Sojojin Isra'ila Sun Ƴanto Palasɗinawan Da Suka Kama A Arewacin Gaza.


Daga - Mahadi Tukur Almizan 

Aƙalla sojojin Isra'ila uku suka tafi jahannama a sakamakon abubuwan fashewa da dakarun rundunar Qassam Brigade ta ƙungiyar Hamas suka dasa birnin Jabalia dake arewacin zirin Gaza a jiya Litinin 23 December, a cigaba da hare haren da dakarun rundunar ta Qassam Brigade ke kaiwa kan sojojin Isra'ila.


Wasu hotuna da aka wallafa a shafin 'Hebrew' dake kafar Telegram sun nuna yadda jirage kirar 'Helicopter' suka riƙa jigilar sojojin Isra'ila da suka samu raunuka daga Gaza zuwa asibitocin Jerusalem.



Wannan yazo ne a daidai lokacin da dakarun na Qassam Brigade suka fitar da sanarwar hare haren da suka ƙaddamar a arewacin Gaza da sojojin Isra'ila suka yi ma ƙawanya tsawon sama da watanni biyu a yunƙurin share Palasɗinawa da jefa su cikin yunwa a yankin na arewacin Gaza.


"A wani hari da wani adadi na Mujahidan mu suka kai sun yi nasarar kashe sojin Isra'ila uku wadanda aka baiwa alhakin tsare wani gida da sojin Isra'ila suka ɓoye a ciki" wani bangare na sanarwar da Qassam Brigade suka fitar a jiya Litinin ɗin.



Sanarwar ta kara da cewa dakarun na Qassam Brigade sun shiga cikin gidan bayan kashe masu tsaron sun kashe dukkanin dakarun sojin Isra'ila dake cikin gidan kuma sun ƙwace makaman su, sun ƴanto wani adadi na daga Palasɗinawan da sojin na Isra'ila suka tsare a wannan gida dake Beit Lahia a arewacin zirin Gaza.


A cikin sanarwar ta rundunar Qassam sun bayyana cewa sun aiwatar da wasu hare hare bayan wannan a jiya Litinin ɗin wanda ya haɗa da dasa abubuwan fashewa da tarwatsa ababen hawa na sojojin Isra'ila da harar sojojin da suka ɓoye a gine gine dake arewacin Gaza.


Hakanan kuma dakarun na Muqawama sun harbo wani ƙaramin jirgi maras matuƙi a wani sabon unguwar 'New Camp' dake tsakiyar Nuseirat ta Gaza.


Wani rahoto da wata kafar yada labarai dake wallafa labarai cikin yaren Hebrew Mai suna Walla ta wallafa cewa rundunar Qassam ta ɗebi sababbin dakaru da adadin su yakai 4,000 wato sababbin ƴan Muqawama da zasu yaƙi  sojin Isra'ila a Gaza.


Suma dai sauran rundunonin muqawama na Palasɗinawa na cigaba da ƙaddamar da hare hare kan sojin na Isra'ila.


Domin itama rundunar Quds da ake kira 'Quds Brigade' a jiya Litinin ta fitar da sanarwa cewa "Mun tarwatsa gungun sojojin Isra'ila da motocin su a wani yunƙuri da suka yi na kutsawa Al-Mabhouh dake sansanin gudun hijira na Jabalia dake arewacin Gaza".

Post a Comment

Previous Post Next Post