Offline

Rigimar Cikin Gida A Isra'ila: Netanyahu Na Fuskantar Barazana A Shari'ar Da Yake Fuskanta A Cikin Gida



Daga - Mahadi Tukur Almizan 

Sakamakon Wasu Bayanai Da Suka Fita Ta Hannun Tsohon Mataimakin Shi Na Musamman 


Firaministan haramtacciyar ƙasa na fuskantar babbar barazana a shari'ar cin hanci da rashawa da yake fuskanta a wadda za a koma kotu a cigaba da shari'ar a mako mai zuwa.


An tuhumi tsohon mataimakin Netanyahu na musamman mai suna Eli Feldstein sakamakon fitar da wasu muhimman takardu da suka ƙunshi muhimman bayanan tsaro (top-secret intelligence document), an zarge shi da miƙa ma kafafen yaɗa labaran ƙasashen ƙetare.


Hukumar watsa labarai ta Isra'ila (KAN) ta labarto cewa Eli Feldstein ya bayyana cewa ya sanar da Firaministan kafin ya fitar da bayanan.


Sai dai Netanyahu ya bayyana cewa baisan da wannan batu ba kawai ya tsinci bayanan ne suna yawo a kafafen yaÉ—a labarai.


Sai dai KAN ta labarto cewa Feldstein yace kwanaki biyu kafin ya fitar da bayanan ya sanar da Netanyahu kafin ya miƙawa kafar yaɗa labarai ta kasar Germany mai suna 'Bild Newspaper'.


Hakanan kuma an wallafa bayanan na sirri a 'Jewish Chronicle' dake ƙasar Birtaniya wato Uku.


Duka kafafen biyu sun wallafa waÉ—anann bayanan sirri, sai dai daga baya kafar yaÉ—a labarai ta Jewish Chronicle ta janye rahoton.


An kama Feldstein ne tare da wasu jami'ai 4 da ake tuhuma da fitar da bayanan sirri da baiwa kafafen yaɗa labarai na ƙasashen waje, a ranar 3 ga watan Nuwamba da ya fita.


Laifukan da ake tuhumar shi sun hada da, tura muhimman bayanai, karbar wasu abubuwa na musamman da aka ɓoye, da kuma haɗin kai domin aikata laifin tare da wasu.


Takardar kotun ta bayyana cewa an sati waÉ—annan bayanai ne daga taskar na'urar bayanai ta sojin Isra'ila, wanda hakan ya haifar da cikas ga yunkurin da Isra'ila take na dawo da mutanen ta dake hannun Hamas.


An bayyana cewa takardun da aka fitar sun ƙunshi bayanan yadda Shaheed Yahya Sinwar ya shirya fitar daga kamammun na Isra'ila daga zirin Gaza, kamar yadda kafafen yaɗa labaran biyu na Germany da Burtaniya suka wallafa, sai dai daga baya kafafen yaɗa labarai na Isra'ila sun bayyana cewa lallai babu gaskiyar samuwar wasu bayanai masu kama da wannan.


Tsagin ƴan adawa na Isra'ila sun tuhumi ofishin Netanyahu da fitar da wannan ƙirƙirarrun bayanai domin kawo cikas ma tattaunawar tsagaita wuta da ake yi da Hamas a Gaza da batun musayar fursunoni.


Sun kuma zargi Netanyahu da ƙoƙarin tsawaita wannan yaƙi domin ya cigaba da zama a kan karagar mulkin ƙasar duk da tuhume tuhumen cin hanci da rashawa da yake fuskanta.


An saka ranar 10 ga wannan wata na December ne a matsayin ranar da za a cigaba da yin shari'ar ta cin hanci da rashawa da ake tuhumar Netanyahu bisa wasu kararraki 3 da aka shigar tun shekarar 2019.

Post a Comment

Previous Post Next Post