Offline

Aƙalla Palasɗinawa 100 Suka Yi Shahada A Hare Haren Isra'ila Jiya Asabar A Gaza

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan 

Daga Asubahi zuwa dare na jiya Asabar aƙalla Palasɗinawa 100 suka rasa rayukansu ciki har da masu aikin bada agaji da ƴan jarida.


Aƙalla Palasɗinawa 40 suka yi shahada a wani hari da Isra'ila ta kai inda Palasɗinawa sama da 100 suka samu mafaka a Tel al-Zaatar dake arewacin Gaza.


👉

Kafafen yada labarai na cikin gida sun bayyana cewa haryanzu akwai mutane da suka maƙale a baraguzan gini saboda ƙarancin ma'aikatan hukumar agaji ta Civil Defense.


Hakanan an samu rahotannin faruwar makamantan wannan hari a Jabalia da Beit Lahia dake makotaka da arewacin Gaza, inda anan ma akwai mutane dayawa da gidajen su suka danne suna ƙarƙashin baraguzan gini tsawon kwanaki biyu da suka wuce, sakamakon hare haren Isra'ila.


Wancan harin na ƙarshe da Isra'ila ta kai zirin Gaza ne ya cika adadin shahidan ya kai aƙalla 100 a jiya kawai.


Tun da sanyin safiyar jiya Asabar ɗin ne sojin Isra'ila suka tarwatsa motar dake ɗauke da ma'aikatan ƙungiyar agaji ta "World Central Kitchen (WCK) NGO, inda suka kashe mutum 4 daga ciki.


👉


Ƙungiyar ta WCK suna sanar a jiya Asabar ɗin cewa za ta dakatar da ayyukan ta a Gaza a karo na biyu a cikin wannan shekara, kamar yadda ta yi a watan Afrilu lokacin da jirgi maras matuƙi na Isra'ila ya jefa ma motar su Bom wanda ya kashe ma'aikatan su da dama na ƙasashen waje.


Har wayau an sake samun rahoton wasu hare haren Isra'ila a Zirin na Gaza, kamar harin da suka kai Khan Younis dake kudanci inda suka kashe Palasɗinawa 17, ciki har da ma'aikacin ƙungiyar agaji ta 'Save The Children' Mai suna Ahmad Faisal Isleem al-Qadi tare da matar shi da ƴar su mai shekaru 3.


👉

Hakanan kuma sojin na Isra'ila sun kashe ɗan jarida ma'aikacin gidan talabijin na Al-Aqsa Tv mai suna Mamdouh Qunaita a wani hari da suka kai asibitin 'Baptist Hospital' dake kudancin Gaza da jirgi maras matuƙi.

Post a Comment

Previous Post Next Post