Daga - Mahadi Tukur Almizan
Dakarun Ansarullah na Yemen da ƴan Muqawama na Iraqi sun hari arewaci da yammacin Isra'ila.
A ranar Talata dakarun ƙungiyar Ansarullah na Yemen sun sanar da cewa sun kai hare hare mabanbanta tare da dakarun muqawama na Iraqi wato 'Islamic Resistance in Iraq' (IRI) a cigaba da nuna goyon bayan Palasɗinu.
"Dakarun Ansarullah da na IRI sun ƙaddamar da hare hare uku kan Isra'ila cikin awanni 48" cewar mai magana da yaqin dakarun gwamnatin Yemen Birgediya Janar Yahya Saree.
بيان القوات المسلحة اليمنية بشأن تنفيذ ثلاث عمليات عسكرية بالاشتراك مع المقاومة الإسلامية في العراق ضد أهداف للعدو الإسرائيلي في شمال فلسطين المحتلة وفي منطقة أم الرشراش جنوباً. pic.twitter.com/p1csGZJGOq
— أمين حيان Ameen Hayyan (@AmeenHa2024yan) December 3, 2024
Hare haren sune:
An kai hare hare biyu arewacin Palasɗinu da Isra'ila ta mamaye, shi kuwa hari na uku ya sauka Umm al-Rashrash dake Eilat ta hanyar amfani da jirage marasa matuƙa.
"Zamu cigaba da kai ma Isra'ila hare hare tare da ƴan muqawama na Iraqi sakamakon ta'addancin da take aikatawa kan ƴan uwan mu a zirin Gaza" wani bangare na bayanan da dakarun na Yemen suka fitar, kuma sun ƙara da cewa "Waɗannan hare hare ba zasu dakata ba har sai an dakatar da ta'addanci kan al'ummar zirin Gaza ".
Tun bayan da aka zartar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Lebanon a watan da ya gabata, dakarun sojin Yemen sun cigaba da kai hare hare Isra'ila, wanda ko a ranar Lahadi Isra'ila ta sanar cewa tayi nasarar kakkabe makaman da dakarun na Yemen suka harba.
Kuma a wannan ranar ne dakarun na Yemen suka sanar cewa sun hari jirgin yaƙi na ruwa da wasu jirage uku masu safarar makamai da jirage marasa matuƙa, duka mallakar Amurka.
