Offline

Isra'ila Za Ta Girke Bindigu Masu Sarrafa Kan Su A Hasumiyoyin Tsaro A West Bank



 Daga - Mahadi Tukur Almizan 

Isra'ila ta ɗauri aniyar samar da fasahar zamani na daga na'urorin tattara bayanai da makamai masu sarrafa kansu da za ta dasa a yammacin gaɓar kogin Jordan.


A yau Lahadi ne Rediyon sojin Isra'ila ya kawo rahoton cewa rundunar sojin Isra'ila ta shirya tsaf domin dasa Bindigu masu sarrafa kansu waÉ—anda zasu iya tantance mutanen da suke so su kashe  a yammacin gaÉ“ar kogin Jordan da suka mamaye, duk da cewa makamantan waÉ—annan makamai da na'urori basuyi nasarar daÆ™ile harin 07 Oktoba ba a baya.


Rahotanni sun nuna cewa ana kan ƙera na'urorin da bindigun da aka ƙera domin a dasa a West Bank.


Kuma za a yi ma jami'an sashe na 636 na rundunar sojin Isra'ila horo na musamman kan sarrafa wannan fasaha, wannan sashe shi aka É—ora ma alhakin kula da sarrafa wannan sabuwar fasaha da ta haÉ—a Bindigu masu sarrafa kansu da hasumiyoyin tsaro (Surveillance Towers).


Rahoton Rediyon sojin Isra'ila ya bayyana cewa Isra'ila na shirye shiryen dasa sabuwar fasahar da ta kira "See-Shot System" a West Bank, wadda kamfanin ƙera fasahohin tsaro mai suna "Rafael Advanced Defense System" ya ƙera ma Isra'ila, wannan fasaha ta ƙunshi na'urorin hasumiyoyin tsaro da bindigu da ake sarrafawa ta hanyar Remote wato 'Remote Control firing mechanism wadda sojojin Isra'ila mata za su rika sarrafawa daga Observation Unit.


An tsara wannan fasaha ne ta yadda zata harbe duk wanda ya kusanci shingen iyakar Isra'ila madamar akwai makami a tare dashi.


Na'urar da aka kira 'Twin turrets' taɓa ɗauke da Camera da kuma bindiga, ita za a dasa a kan hasumiyoyin tsaro a West Bank ɗin, kuma ba za a ajiye sojojin a wurin ba iya makaman ne kawai su kuma sojojin zasu yi zaman su a cikin hasumiyoyin ne suna sarrafa makaman ta hanyar amfani da Remote.


Wannan dai ba shi ne karon farko da Isra'ila za ta yi amfani da wannan fasaha ba, domin kuwa tun 2008 take amfani da wannan fasaha a zirin Gaza, sai dai wannan bai hana afkuwar harin 07 Oktoba ba da ya taso daga Gaza.


Wannan yasa wani wakilin gidan Rediyon sojin na Isra'ila ya nuna damuwar shi akan wannan fasaha inda ya bayyana cewa "Fasahar da ta batayi  nasara ba a Gaza, tayaya zamu yi tsammanin zata yi nasara a West Bank?".


Sai dai kafar Rediyon ta bayyana cewa an É—auki wannan mataki na dasa fasahar ne saboda yawan samun hare hare da ake kaiwa matsugunan Æ´an share wuri zauna ne.

Post a Comment

Previous Post Next Post