Daga - Mahadi Tukur Almizan
Hukumar ta Palasɗinawa wato 'Palestinian Authority' wadda Mahmud Abbas ke yi ma jagoranci ta yi haɗaka da Isra'ila wajen kai hari sansanin ƴan gudun hijira na Jenin dake yammacin gaɓar kogin Jordan da sunan ƙoƙarin dawo da doka da oda a sansanin.
Dakarun Palestinian Authority sun ƙaddamar da wani hari da sanyin safiyar shekaran jiya Asabar 14 December a sansanin na Jenin, a wannan hari da suka kai sun kashe kwamandan rundunar ƴan Muqawama na Jenin "Jenin Brigade Commander" Mai suna Yazid Ja'ayseh, wannan runduna wani reshe ne na rundunar "Quds Brigade" ta ƙunshi 'PIJ' wato 'Palestinian Islamic Jihad's.
Mai magana da yawun dakarun hukumar ta Palasɗinawa 'PA' (Palestinian Authority) Birgediya Janar Anwar Rajab ya bayyana cewa wannan harin haɗaka ne da sojojin Isra'ila kuma sun kai harin ne "Domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya, da kuma samar da dokoki domin kawo karshen tashin hankali a sansanin". A cewar shi.
The Palestinian Authority's (PA) Security Forces launched an assault today on the Jenin refugee camp, in the occupied West Bank, to pursue and assassinate resistance fighters.
— The Cradle (@TheCradleMedia) December 14, 2024
Spokesman Brigadier General Anwar Raja said that the operation aimed at "preserving security and civil… pic.twitter.com/bNZsR0AQnU
Rajab ya ƙara da cewa manufar fadar mulki ta Ramallah da Tel Aviv (yana nufin gwamnatin su ta PA da gwamnatin Isra'ila) shine "Dawo da doka da oda, sakamakon rashin doka da ya jefa fararen hula dake rayuwa a sansanin cikin ƙuncin rayuwa, kuma ya hana su yin rayuwa cikin ƴanci da zaman lafiya".
A wannan hari da suka kai shekaranjiya Asabar, harsasan da dakarun na Palestinian Authority suka harba ya kashe wani ƙaramin Yaro mai suna Mohammad al-Amer
The child Mohammad al-Amer has been murdered by the bullets of the Palestinian Authority's (PA) security forces in the occupied West Bank city of Jenin.
— The Cradle (@TheCradleMedia) December 14, 2024
This comes after the PA launched an assault on Jenin Camp and its resistance fighters in coordination with Israel. pic.twitter.com/cF7INLoaSB
Sai ƙungiyoyin ƴan Muqawama na Palasɗinawa sun yi Allah wadai da wannan hari.
Ƙungiyar PIJ (Palestinian Islamic Jihad's) ta bayyana cewa " Harar ƴan Muqawama da PA ta yi a Jenin yayi daidai da ayyukan ta'addancin da Isra'ila ke yi kan al'ummar Palasɗinu".
Ita ma ƙungiyar Hamas ta bakin jami'in ta mai suna Abdul-Rahman Shadeed ya yi Allah wadai da wannan aika aika ta PA, inda ya bayyana cewa fadar mulki ta Ramallah ba kokarin haddasa rikicin cikin gida ne da wannan aika aikar, kuma dole ne ta dakatar da hakan.
Ya kara da cewa Palestinian Authority dole ne ta tsayu wajen cigabantar da ƙasar Palasɗinu ne baki daya ba ƙoƙarin harar shugabannin Muqawama ba a West Bank, yayi wannan zantuka ne a yayin da yake zantawa da kafar yaɗa labarai ta Aljazeera.
Wannan hari na ranar Addabar yazo ne bayan kwanaki 5 da PA ta yi ma sansanin na Jenin ƙawanya wai da sunan kare ƙasa kamar yadda Rajab ya bayyana.
🎥| Elite armed forces of the Palestinian Authority (PA) equipped with sniper rifles & armored jeeps, doing Israel’s dirty work in Jenin—they operate with the official consent of Israel. pic.twitter.com/hFgOkW2vB4
— Arya - آریا (@AryJeay) December 9, 2024
A dai dai lokacin da dakarun PA suka yi ma Jenin ƙawanya su kuma dakarun Isra'ila suna cigaba da kai hare hare a yammacin na gaɓar kogin Jordan daga ranar juma'a zuwa jiya sun kashe Palasɗinawa 15 a tsakanin Ramallah, Tulkarem , Hebron, Jenin da Jerusalem.
