Offline

Hare Haren Isra'ila Sun Shahadantar Da Aƙalla Palasɗinawa 70 A Zirin Gaza A Jiya Laraba



Daga - Mahadi Tukur Almizan 

Sabbin hare haren da Isra'ila ta gabatar a muhallan da al'ummar Palasɗinu suka samu mafaka sun yi sanadiyyar shahadar sama da mutum 50 a fadin zirin Gaza.


Aƙalla Palasɗinawa 20 aka kashe a wani sabon hari a sansanin gudun hijira na Al-Mawasi dake yammacin birnin Khan Yunis dake kudancin Gaza a yau ajiya Laraba 4 ga wannan wata na December.



Hukumar agaji ta Palasɗinawa 'Palestinian Red Crescent ' ta fitar da rahoton cewa jirgin saman yaƙi na Isra'ila ya hari tantunan Palasɗinawa da suka rasa muhallan su da wuraren ajiye abinci "Ƴan mamayar suna sani cewa fararen hula ne suka hara domin sun ƴan gudun hijira ne kawai a sansanin na Mawasi" cewar mai magana da yawun hukumar Civil Defense ta Gaza Mahmoud Basal yayinda yake zantawa da kafar yaɗa labarai ta Aljazeera.


Al-Mawasi dai sansani ne da aka tanada a matsayin tudun mun tsira da Palasɗinawa zasu fake, kuma Isra'ila ce ta samar da shi sakamakon matsi daga ƙasashen duniya, wannan sansani yana daga cikin sansanoni da suke dauke da adadi mafi yawa na mutane a Gaza, sama da mutum miliyan 2 suka tare a lokaci ɗaya a sansanin.


Wannan sansani ya fuskanci hare haren Isra'ila aƙalla sau 8 daga watan May zuwa jiya wanda ya bar ɗaruruwan mutane da raunuka.


Sojin Isra'ila sun cigaba da kai hare hare kan Palasɗinawa dake gudun hijira a faɗin zirin Gaza inda suka kashe aƙalla mutum 70 daga Asubahin ranar Laraba.


Aƙalla Palasɗinawa 10 suka kashe a birnin Gaza, inda suka buɗe wuta a unguwannin fararen hula abinda suka kira "Belf of fire operation". Hakanan kuma sun kashe wasu mutum 5, huɗu daga cikin su ƙananan Yara ne wanda aka kashe ta hanyar amfani da jirgi maras matuƙi a sansanin gudun hijira na al-Nuseirat Camp.




Hare haren sun faɗaɗa zuwa arewacin Gaza, inda acan ma sojin na Isra'ila suka aiwatar da munanan hare hare, kuma suka tursasa mutane barin muhallan su.


Sojin na Isra'ila sun tursasa mutane barin muhallan nasu a Beit Lahia dake arewacin Gaza, inda suka riƙa amfani da amsa kuwwa (Loudspeaker) da jirgi maras matuƙi suna sanarwa kamar yadda ɗan jarida Anas al-sharif ya labarto a daren jiya Laraba.


Duk da haka a cikin dare anji fashewar abubuwan fashewa a Beit Lahia sakamakon abubuwan fashewa da sojin na Isra'ila suka binne domin tarwatsa sauran iyalan da suka rage a unguwar.




Hukumar Civil Defense ta Gaza ta bayyana cewa a halin yanzu aƙalla Palasɗinawa dubu 60 ke fuskantar barazanar mutuwa sakamakon mummunan yanayin da aka shiga a Beit Lahia.


Shima asibitin Kamal Adwan dake arewacin Gaza ta fuskanci hare haren sojin Isra'ila a jiya Laraba, wanda ya haddasa aka rasa iskar Oxygen gaba ɗaya a asibitin.


Jirage marasa matuƙa sojin Isra'ila suka riƙa amfani da su wajen jefa ma duk wanda ya motsa gurneti (grenade) kamar yadda shugaban asibitin ya bayyana ma manema labarai Dr. Hussam Abu Safia a ranar Talata.



Post a Comment

Previous Post Next Post