Daga - Mahadi Tukur Almizan
Sojin Isra'ila na cigaba da kai hare hare a makarantun da Palasɗinawan da suka rasa gidajen su ke zaman neman mafaka a zirin Gaza.
A jiya Litinin 16 ga watan December ma'aikatar lafiya ta Palasɗinawa ta fitar da sanarwa cewa Palasɗinawa 52 Isra'ila ta kashe tare da raunata wasu sama da 200 a zirin Gaza cikin awa 24.
"Sojojin mamaya sun aikata kisan kare dangi kan ahali 7 a zirin Gaza, wanda yayi sanadiyar shahadar mutum 52 tare da raunata mutum 203 a cikin awanni 24 da suka gabata" - rahoton na ma'aikatar lafiyar.
Ma'aikatar ta ƙara da cewa daga 07 na shekarar 2023 zuwa yau Isara'ila ta kashe Palasɗinawa 45,028 cewar shugaban ƙungiyar 'Palestinian NGO Network' Ahmad Shawa yayin da yake zantawa da kafar yaɗa labarai ta Aljazeera, ya kara da cewa adadin zai iya zarce haka sakamakon haryanzu akwai wasu a ƙarƙashin baraguzan gini da kuma waɗanda suka ɓata.
Isra'ila dai ma cigaba da kai munanan hare hare babu ƙaƙƙautawa a faɗin zirin Gaza a kowace rana.
Ko a ranar Lahadi 15 ga December sun kashe Palasɗinawa 15 tare da raunata wasu a wani hari da sojin Isra'ila suka kai ta sama kan gungun Palasɗinawa fararen hula a sansanin gudun hijira na Al-shati dake yammacin birnin Gaza.
Hakanan kuma a daren da ya gabaci wannan ranar sun kashe mutum 20 tare da jikkata wani adadi mai yawa lokacin da suka jefa Bom a makarantar Ahmad Bin Abdul'aziz da Palasɗinawa suke zaman a ciki sakamakon rasa gidajen su da suka yi a kudancin birnin Khan Yunis.
Sojojin na Isra'ila sun afka makarantar Khalil Oweida wadda wasu Palasɗinawa ke zaune dake Beit Hanoun a arewacin Gaza inda suka je suka buɗe wuta da sanyin safiyar shekaranjiya 15 ga wata suka kashe aƙalla mutum 40 kuma suka tilasta mutane barin muhallan su, hakanan kuma sun kwashe dukkanin Mazan da suke zaune makarantar ta Khalil Oweida dake Beit Hanoun ɗin.
Ana dai ganin waɗannan ƙazaman hare hare Isra'ila a matsayin yunkurin share Palasɗinawa daga arewacin Gaza da suka yi ma laƙabi da "General Plan"
