Daga - Mahadi Tukur Almizan
A ƙalla ƴan share wuri zauna 9 ne suka samu raunuka, uku daga cikin su na cikin mummunan yanayi
Tsagin dakarun ƙungiyar Hamas da ake kira "Qassam Brigade" sun ɗauki alhakin wani hari da akai kai yammacin gaɓar kogin Jordan a jiya juma'a 29 November inda aka hari ƴan share wure zauna.
The toll has risen to nine settlers injured, including three in critical condition, in a shooting operation outside the colonial Israeli settlement of Ariel in the occupied West Bank. The executor of the operation was subsequently shot dead by Israeli occupation forces. pic.twitter.com/lDmtXwR3IZ
— Quds News Network (@QudsNen) November 29, 2024
Qassam Brigade sun sanar da alhakin wannan hari da aka buɗe wuta a yankin Salfit dake arewacin yammacin gaɓar kogin Jordan, inda wani Mujahidi ya ƙaddamar da harin ban mamaki kan Sahayuniyawa sojoji da ƴan share wuri zauna dake cikin wata motar Bus, inda ya raunata 9, uku daga cikin suna cikin mummunan yanayi, lamarin ya faru ne da tsakiyar rana a jiya juma'a, cewar Qassam Brigade.
👉
Shooting Attack Near Ariel Leaves Nine Israeli’s Injured
— News is Dead (@newsisdead) November 29, 2024
Nine Israeli’s were injured, three critically, in a shooting attack on a bus near the Ariel settlement in the northern West Bank. The attacker opened fire at a busy junction before being killed by Israel’s forces.
This… pic.twitter.com/MUvDySpclY
Rundunar ta Qassam ta bayyana cewa an dauki matsayar kai wannan hari ne sakamakon hare haren ta'addancin da Gwamnatin Sahayuniyawa ke kaiwa yammacin gaɓar kogin Jordan, kuma zasu biya farashin wannan aika aikar ne da jinanen sojojin su da ƴan share wuri zauna dake yammacin gaɓar kogin Jordan ɗin.
Mahairin ya hari wata babbar motar Bus ne wadda ke cike da ƴan share wuri zauna, ya buɗe masu wuta hakan yayi sanadiyyar raunata mutane tara wanda a cikin su ne uku ke cikin mawuyacin hali, a cikin masu raunukan akwai sojoji.
Maharin da ya kai harin shine Samer Mohammed Ahmed Hussein, sojin Isra'ila sun harbe shi nan take yayi shahada.
Bayan aukuwar wannan harin shugaban matsugunan ƴan share wuri zauna na Kedumim ya bayyana cewa "Yanzu ne lokacin da za a shiga yammacin gaɓar kogin Jordan ya share Palasɗinawa daga doron duniya".
Daga bayanan da ake samu daga ɓangaren sojin Isra'ila, akwai ƙoƙarin da wasu suke ta yi na matsawa kan a mayar da yammacin gaɓar kogin na Jordan babban filin daga a wannan yaƙi.
Tun a watan August dai Isra'ila ta ƙaddamar da mamayar yammacin gaɓar kogin Jordan da hare hare babu kaƙƙautawa, tun wannan lokacin suke cigaba da afkawa ƙauyuka da kama mutane , sun kashe fararen a biranen yammacin gaɓar kogin na Jordan da sansanonin gudun hijira wuraren da masu alaƙa da Hamas da PIJ (Palestinian Islamic Jihad) suke da ƙarfi.
Sama da Palasɗinawa 700 Isra'ila ta kashe a yammacin gaɓar kogin Jordan (West Bank) daga 07 Oktoba na shekarar 2023 zuwa yau.

